in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rashin isasshen barci na iya sanya mutane su kamu da mura cikin sauki
2016-01-11 08:15:10 cri

Bincike ya nuna cewa, samun isasshen barci yana taimakawa wajen kasancewa cikin koshin lafiya! Wani nazari da masana daga kasar Amurka suka wallafa a cikin mujallar "Barci" ta Amurka a kwanan baya ya sake tabbatar da cewa, mutanen da ba su samun barci na tsawon sa'o'i 6 a ko wace rana suna fuskantar barazanar kamuwa da mura sannan kuma barazanar ta ninka sau 4 ko fiye da haka gwarwadon mutanen da su kan yi barci fiye da sa'o'i 7 a ko wace rana.

Masu nazarin sun fahimci cewa, barci yana kara koshin lafiya. Sannan akwai alaka a tsakanin rashin isasshen barci, saukin kamuwa da ciwo, yiwuwar kamuwa da cutar dake addabar mutum sannu a hankali, da mutuwar kuruciya, haka kuma rashin isasshen barci kan haddasa illa kan amfanin allurar rigakafi.

Masu nazari daga reshen jami'ar San Francisco dake California a Amurka sun gudanar da wani bincike kan masu aikin sa kai dari 1 da 64, inda suka matsin lambar da wadannan masu aikin sa kai suke fuskanta, halayyarsu, ko suna shan taba ko giya ko a'a. Daga baya masu nazarin sun bukaci wadannan masu aikin sa kai su sanya wata na'urar musamman a hannunsu domin rubuta tsawon lokacin da suka kwashe suna barci a ko wane dare da nauyin barci da masu aikin sa kan suka yi. Bayan mako guda, an gayyaci wadannan masu aikin sa kai zuwa wani otel, inda aka saka musu kwayoyin cutar mura a jikinsu, kana aka yi nazari a kansu na tsawon mako guda.

Sakamakon nazarin ya shaida cewa, in an kwatanta mutanen da su kan yi barci na fiye da sa'o'I 7 a ko wane dare, barazanar da mutanen ke fuskanta ta kamuwa da mura da tsawon lokacin barcinsu bai kai sa'o'I 6 a ko wane dare ba,wato ya ninka sau 4.2, kana kuma, irin wannan barazanar da mutanen ke iya fuskanta da tsawon lokacin barcinsu bai kai sa'o'I 5 a ko wane dare ba,ma'ana ya ninka sau 4.5.

Masu nazarin suna ganin cewa, yayin da ake hasashe game da barazanar da mutane ke fuskanta ta kamuwa da mura, abu mai muhimmanci da ake la'akari su ne rashin isasshen barci, shekarunsa na haihuwa, matsin lambar da yake fuskanta, matsayin ilminsa, yawan kudin shigarsa, da ko yana shan taba ko a'a.

Wannan sabon sakamakon nazari shi ma ya kara tabbatar da cewa, kamata ya yi a ba da muhimmanci ga samun isasshen barci yayin da ake kokarin kasancewa cikin koshin lafiya kamar yadda ake mai da hankali kan cin abinci yadda ya kamata da kuma motsa jiki ta hanyar da ta dace. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China