in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwayoyin cuta dake taruwa a kasan hakora na iya haddasa yaduwar cutar mura
2016-01-31 11:10:10 cri

A kwanakin baya ne, wasu manazarta a kasar Japan suka gano cewa, kwayoyin cutar dake makalewa a karkashin hakora na iya haddasa yaduwar kwayoyin cutar dake haifar da cutar mura a jikin Adam. A don haka yana da kyau a mai da hankali wajen tsabtace baki, kuma hakan zai iya zama tamkar yin rigakafi ne daga kamuwa da cutar mura.

Masu bincike daga jami'ar Nihon ta Japan sun bayyana cewa, wasu kwayoyin cutar da ke bakin dan Adam suna iya raunana amfanin magungunan yaki da cutar mura kamar Tamiflu, wasu kuma kan haddasa karuwar yaduwar kwayoyin cutar ta mura.

Yayin da kwayoyin cutar mura suka shiga cikin kwayoyin halittu na jikin dan Adam, ba lallai ne su iya yaki da sauran kwayoyin halittu na jikin mutum ba, sai dai sakamakon wani nau'in sinadarin da ke wajen kwayoyin halittu na jikin dan Adam, ya sa nau'in furotin din da ke wajen kwayoyin cutar mura ya sauya, don haka kwayoyin cutar mura na iya samun kwarin gwiwa na ci gaba da kama sauran kwayoyin halittu na jikin bil Adama.

Masu nazarin sun yi bincike kan kwayoyin cutar mura mai nau'in A-H3N2. Kuma sun gano cewa, irin wannan kwayoyin cuta na iya ci gaba da kama sauran kwayoyin halittu na jikin dan Adam, sakamakon wani nau'in sinadarin da ke cikin kwayoyin halittu na kayayyakin jiki masu taimakawa wajen gudanuwar numfashi. Bayan da masu nazarin suka sa wani nau'in kwayar cutar da ta kan haddasa cutar gindin hakora a cikin kwayoyin halittu na jikin dan Adam, da kuma kwayoyin cutar murar, sun gano cewa, irin wannan kwayar cutar da ta kan haddasa cutar gindin hakora ita ma tana iya karfafa karfin kwayoyin cutar mura mai nau'in A-H3N2 su ci gaba da kama sauran kwayoyin halittu na jikin dan Adam.

Sakamakon nazarin ya shaida cewa, ya zama tilas a mai da hankali kan tsabtar baki a matsayin hanyoyin yaki da cutar mura.

Masu nazarin na Japan suna ganin cewa, karfin tsoffafi na yin rigakafin kamuwa da cututtuka yana raunana, idan har ba su kula da lafiyar bakinsu yadda ya kamata ba, to, da zarar kwayoyin cutar mura suka kama su, cikin sauki cutar zata iya yin illa gare su. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China