Maganar da saban ministan harkokin matasa da wasanni na taraiyar Nigeria mr. Saloman Dalung ya yi na cewa, gwamnatinsu ta amunce za ta fara ba wa matasan Nigeria kudin tallafi 5,000 a duk wata tare da koya wa matasan wasu sana'o'in hannu wanda zai taimakawa matasan su dogara da kansu, hakika wannan kyakkyawar aniya ce kuma abun koyi ga sauran kasashenmu na Afirka wayanda suka yi watsi da bukatar matasan kasashensu inda matasan ke yin tururuwa ayari-ayari tare da yin rigegeniya zuwa kasashen nahiyar yin ci-rani dan neman abun yi da kuma samun rayuwa mai inganci inda galibi matasan ke rasa rayukansu. A nawa ra'ayin, tallafa wa matasa wani ginshiki ne na inganta rayuwar matasa kuma wata dama ce ta kawo bunkasuwar tattalin arziki da kuma samar da zaman lafiya mai daurewa. Da wannan nake kira ga sauran kasashenmu na Afirka da su yi koyi da saban shirin tallafa wa matasa da gwamnatin madugun chanji shugaban kasa Buhari ya kirkiro karkashin ma'aikatar kula da harkokin matasa da wasanni ta kasa dake birnin taraiyar Nigeria Abuja.
Daga Alhaji Ali kiraji Gashua.