in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masu kiba sun fi saurin yin tunani, kana suna da saurin mantuwa
2015-12-06 10:06:24 cri

A zamanin yau, ana danganta masu kiba da sauri kamuwa da ciwon hawan jini da wasu matsalolin da suka shafi lafiya. Amma wani sabon bincike ya nuna cewa, akwai bambanci a tsakanin masu kiba da masu madaidaicin nauyin jiki a fannin yadda kwakwalwarsu take yin aiki. Masu kiba sun fi saurin yin tunani,haka zalika suna da saurin mantuwa.

Masu nazari daga jami'ar London ta kasar Birtaniya sun kwashe shekaru 10 suna gudanar da wani bincike kan ma'aikatan gwamnatin kasar dubu 6 da dari 4, wadanda shekarunsu suka wuce 50 amma bai kai 61 ba a duniya. Masu nazarin sun tantance takardun binciken lafiyarsu na tsawon shekaru 10, kamar nauyin jiki, hawan jini, yawan kitsen da ke jikinsu, da tarihin shan magani. Ban da haka kuma, masu nazarin sun yi bincike kan halayyarsu a lokuta daban-daban guda uku a cikin wadannan shekaru 10, inda suka jarraba yadda suke iya tunawa da wasu abubuwa da dai sauransu.

Bayan kammala wannan tantancewa, masu nazarin sun gano cewa, a cikin wadannan ma'aikatan gwamnati, 582, suna da kiba, a cikinsu kuma wasu 350 sun gamu da wasu matsaloli da suka shfai lafiya, kamar hawan jini, ciwon sukari da dai sauransu. A cikin shekaru 10, wadanda ke da matsalar kiba sun gamu da matsalar mantuwa da ta tunani, musamman ma wadanda suke fama da ciwon hawan jini, matsalar yawan kitse da ke jiki da ciwon sukari, kwarewarsu ta fahimta ta gamu da matsala.

Dangane da sakamakon nazarinsu, masu nazarin sun yi bayani karara cewa, ko da yake ba su san yadda matsalar kiba da kuma matsalar sarrafa sinadaran jiki suke kawo illa ga yadda kwakwalwar dan Adam take aiki ba, amma duk da haka sakamakon nazarinsu ya shafe tsohon tunanin da mutane ke yi cewa, idan har mutum yana cikin koshin lafiya, to, ba ba zai yi wani kiba ba. Hakika, sakamakon nazarce-nazarce da aka yi a baya sun taba ba da shawara, alal misali, kamata ya yi matsakaitan mutane su rika cin abinci mai gina jiki, motsa jiki da yawa, su nisanci shan taba, kana su rika sa ido kan hawan jini da yawan kitsen da ke jiki, hakan zai taimaka wajen yin rigakafin kamuwa da matsalar toshewar basira dake da nasaba da tsofaffi da kuma ta'azzaran ciwon. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China