Tare da fatan baki dayan ma'aikatan ku suna cikin koshin lafiya a birnin Brijing kamar yadda na ke lafiya a nan Kano. Bayan haka, bisa la'akari da matsalar rashin karfi da kyan sauti yayin gabatar da shirye shiryen ku na safe, ina ba ku shawara domin ku fara maimaita shirukan ku na safe da yammaci musamman shirin karfe 7:00 zuwa 7:30 na yammaci kan mita 25 (11640khz), wanda mu ke iya sauraro rangadadau.
Hakika, shirye shiryen da ku ke gabatarwa da safe suna da fa'ida wajen nishadantarwa, musamman shirin Kide kiden kasar Sin, da Dandano jiran Rabo, da Kide kiden kasar Indiya da Pakistan wadanda ke debe kewar masu sauraro matuka. Saboda haka, maimaita shirukan safe da yammaci karfe 7:00 zuwa 7:30 kan mita 25 ko
(11640khz) ya dace. Da fatan za ku yi nazarin wannan shawara tawa domin duba yiwuwar amfani da ita. Da fatan zumuncin da ke tsakanin mu zai ci gaba da habaka. Na gode.
Mai sauraron ku a kullum
Nuraddeen Ibrahim Adam
Great Wall CRI Listeners' Club
Kanon Dabo, Nigeria