in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jariran da aka shayar da su nonon uwa zalla, da wuya su gamu da matsalar kiba bayan da suka girma
2015-10-28 19:55:57 cri

Masu karatu, idan kuna fatan yaranku su rayu ba tare da yin kiba ba bayan da suka girma, to, ya fi kyau ku shayar da su nonon uwa zalla!

Kwanan baya, jami'ar ilimin likitanci da ilimin hakora ta birnin Tokyo dake kasar Japan, ta gabatar da wani rahoto da ke cewa masu nazarin ta sun gano cewa shayar da jarirai nonon uwa zalla, yana taimakawa wajen karfafa gwiwar kwayoyin dabi'ar halitta masu kula da narkar da kiba a jikin jariran ta yadda zasu yi aiki yadda ya kamata.

Don haka idan aka kwatanta da jariran da ba a shayar da su nonon uwa zalla ba, da wadanda aka shayar da su nonon uwa zalla, kaso na biyu za su yi wuyar gamuwa da matsalar kiba bayan da suka girma.

A cikin rahoton, masu nazarin sun bayyana cewa, dalilin da ya sa haka shi ne domin a cikin nonon uwa, akwai wasu sinadarai na musamman masu tarin yawa, wadanda za su karfafa gwiwar wani nau'in furotin da ke jikin mutum, ta yadda zai taka rawa yadda ya kamata, ya taimakawa kwayoyin dabi'ar halitta masu kula da narkar da kiba a jikin mutum su fara aiki yadda ya dace.

Masu nazarin suna ganin cewa, sakamakon nazarinsu zai ba da taimako wajen lalubo bakin zaren yadda za a taimaka wa jarirai, su yi girma yadda ya kamata, tare da kera nonon da amfaninsa zai kara yin kama da nonon uwa.

Har wa yau kuma, masu nazarin suna ganin cewa, mai yiwuwa ne wasu kwayoyin dabi'ar halitta da ke jikin jarirai, za su tuna da yadda jikin jariran suke kasancewa, hakan zai yi tasiri kan ko wadannan jarirai za su samu saukin kaucewa kiba, ko kamuwa da sauran cututtukan da ke da nasaba da al'adarsu a zaman rayuwa bayan da suka yi girma ko kuma a'a. Sabili da haka ne ma kulawa da yadda jarirai suke cin abinci masu gina jiki yadda ya kamata, zai kasance wani muhimmin batu da masu ilmin likitanci za su yi nazari a kai, a kokarin su na yin rikafin kamuwa da cututtuka. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China