in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ra'ayi na dangane da fara watsa shirin safe
2015-05-18 14:59:53 cri
Zuwa ga sashen Hausa na CRI.

Tare da fatan alheri ga baki dayan ma'aikatan ku, ina fatan duk kuna cikin koshin lafiya a birnin Beijing. Bayan haka, ina mai cike da farin cikin samun labarin cewa, ranar 1 ga watan Yuni na bana, sashen Hausa na CRI zai gabatar da wasu muhimman sauye sauye ta fannin watsa shirukan sa, wato za a fara watsa shirin safe a maimakon shirin yamma da a ka riga aka saba sauraro tare da maimaicinsa a kowacce rana.

Hakika, wannan sauyi bisa la'akari da shawarwarin da masu sauraro suka jima suna gabatarwa ya yi daidai, kuma ya tabbatar da yadda sashen Hausa ke martaba shawarwarin masu sauraron sa tare da yin la'akari da sauye sauyen da zamani ke tafiya da shi. Ko shakka babu, wannan sauyi zai kara armashin aikin watsa labarai na CRI Hausa, domin yanzu masu sauraro za su iya sauraron sabbin shirye shirye har sau biyu a kowacce rana. Kana, wanda ya kuskure sauraron shirin safe yana da damar sake tarawa don sauraron wani sabon shirin da maraice.

Tare da fatan injiniyoyin ku za su kula da batun ingancin sauti yayin watsa shirin naku na safiya don tabbatar da cewa mu na kama tashar ta CRI Hausa rangadadau kamar a shirye shiryen ku na yamma. Ina fatan wannan sauyin watsa shirye shirye zai kara wa sashen na Hausa farin jini da kuma karbuwa tsakanin al'ummar Afirka da ke jin harshen na Hausa. Na gode.

Mai sauraron ku a kullum

Nuraddeen Ibrahim Adam

Great Wall CRI Listeners' Club

Kanon Dabo, Nigeria

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China