Bayan gaisuwa mai yawa tare da fatan alheri da fatan baki dayan ma'aikatan sashen Hausa suna cikin koshin lafiya. Bayan haka, ima farin cikin gabatar mu ku da wata shawara dangane da bukatar kara inganta yanayin shafin yanar gizo na sashen Hausa ta hanyar dora cikakken shirin sa'a guda da a ka saba gabatarwa a kullum kan shafin internet domin bayar da dama ga masu amfani da wayar salula ta zamani da a ka fi sani da, komai da ruwan ka, su rika shiga shafin CRI Hausa kai tsaye suna sauraron shirye shirye.
Ban da wannan, akwai bukatar samar da manhajar shafin yanar gizo wacce za ta ba da zabi ga mai sauraron da ya ziyarci shafin ya saurari cikakken shirin kowacce rana da yake bukata kuma ya sauke shirin da yake so wato (download) idan yana da ra'ayi ko bukatar raba wa ga abokai.
Hakika, miliyoyin mutane musamman a nan Nijeriya suna dogara ne kan wayoyin su na salula wajen sauraron shiryen shiryen kafafen yada labari daban daban, wannan ya taimaka matuka yada labarai da sauran bayanai da su ka shafi rayuwar al'umma ga dimbin mutane. Dangane da haka, ina fatan sashen Hausa zai kalli wadannan shawarwari da idanun basira. Na gode.
Mai sauraron ku a kullum
Nuraddeen Ibrahim Adam
Great Wall CRI Listeners' Club
Kanon Dabo, Nigeria