in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kayyade shigar da calore cikin jikin mutum ba shi da tasiri wajen tsawaita rayuwar mutane
2015-05-30 20:17:27 cri


Kullum mutane na gaskata cewa, kayyade yawan calore da mutane suke shigarwa cikin jikunansu ta hanyar cin abinci, na iya kare mutum daga saurin tsufa, wanda hakan ka iya tsawaita rayuwar mutum. Sai dai wani bincike da wasu masu nazari na kasar Amurka suka kwashe shekaru 20 su na gudanarwa kan wasu dabbobi, ya shaida cewa, ko da yake kayyade shigar da calore cikin jikin mutum yana da amfani wajen inganta lafiyar jiki, a daya hannun hakan ba shi da wani amfani a fannin tsawaita rayuwa.

Yau shekaru fiye da 20 aka shafe a cibiyar nazari game da batun tsoffaffi ta kasar Amurka, ana gudanar da bincike ta hanyar kiwon birai irin na Rhesus guda 121, tare da tantance su.

Biri nau'in Rhesus da kuma dan Adam, sun yi kama da juna ta baki da hancinsu, kuma birin Rhesus na da tsawon rai. Don haka masu nazarin kimiyya suka fi maida hankali ga nazarce-nazarce masu tsawo kan wannan nau'i na birai wato Rhesus.

Masu nazarin dake cibiyar nazarin batun tsoffaffi ta kasar Amurka sun raba wadannan biran Rhesus zuwa rukunoni guda biyu. Sa'an nan suka rika raba masu yawan calore bisa mizani daban daban, wato wani rukuni aka rika ciyar da su calore a ko wace rana, ta hanyar cin abinci da kashi 30 cikin dari, yayin da daya rukunin aka kayyade nau'in abincin su. Bayan shekaru 20 ko fiye da haka, adadin kididdigar da masu nazarin suka samu ya nuna cewa, duk biran Rhesus maza da mata, cikin shekarun da suka kasance a duniya, yayin da aka fara kayyade yawan calore da suke ci, ba su babbanta da rukunoni na 2 na biran Rhesus ta fuskar tsahon rayuwa ba.

Amma duk da haka a hannu guda kuma, wannan bincike ya shaida cewa, ko da yake kayyade yawan calore da wadannan biran Rhesus suka ci bai iya taimakawa wajen tsawaita rayukansu ba, a hannu guda ya tallafa musu wajen inganta lafiyar jikin su.

Kayyade yawan calore da suka shigar jikunansu a ko wace rana ya na iya taimakawa musu rage nauyin jikinsu, kana kuma yawan Cholesterol, da Glycerin Trilaurate da ke jikin mutum yana raguwa. Har wa yau kuma akwai alamar da ke cewa, daukar wannan mataki na iya dakatar da kamuwa da ciwon kansa, da ciwon sukari, da kuma ciwon amosanin gabbai. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China