in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yadda za ka wanke hannunka domin yaki da cutar Ebola
2014-08-15 20:08:20 cri

• A yi amfani da fallen katardar da ake amfani da ita a bayan gida wajen bude kofar fita daga bayan gidan da jama'a ke amfani da shi, maimakon a rika taba abin bude kofar da hannun da aka wanke. Domin ba kowa ba ne yake wanke hannunsa kafin ya fita daga bayan gida.

• A wanke hannu har zuwa gwiwar hannu, musamman idan mutum yana mu'amula da abubuwa masu datti, wannan zai taimaka wajen kawar da kwayoyin cuta a hannun baki daya, duk da cewa, ba koda yaushe muke amfani da baki dayan hannu ba, amma mu kan hade hannunmu waje guda, don haka, wanke baki dayan hannun zai sa ka kasance cikin tsafta har ma da sauran jama'a.

• Kada ka wanke hannu da ruwa kawai. Domin kwayoyin cuta sun fi son zama a wuri mai damshi da dumi, don haka, akwai bukatar ka yi amfani da sabulu wajen kawar da su.

• Idan akwai maiko a hannunka, misali a lokacin da ka canja bakin man motarka, kamata ya yi ka yi amfani da sukari da sabulu ka cuda hannu yadda ya kamata a lokaci da aka zo wankewa, hakan na taimakawa wajen fitar da duk wani maikon da ke jikin hannu cikin sauki.(Ibrahim Yaya)


1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China