in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ina taya al'ummar kasar Sin bikin ranar kafuwar Jamhuriyar kasar Sin
2013-10-01 16:33:51 cri
Zuwa ga sashen Hausa na rediyon kasar Sin,

Bayan gaisuwa mai tarin yawa dafatan dukkanin ma'aikatan Sashen Hausa suna cikin koshin lafiya.

Bayan haka a mamadin 'yan kungiyar Great Wall na masu sauraron CRI muna taya al'ummar kasar Sin bikin ranar kafuwar jamhuriyar kasar Sin wato 1 ga watan oktoba 1949 wanda mu kuma anan Najeriya yai dadai da ranar samun 'yancin kai daga 'yan mulkin mallaka na kasar Biritaniya wato a ranar 1 ga watan oktoba 1960. Don haka wannan rana nada mahimmaci ga mu 'yan Najeriya da kuma Sinawa. Ina Fatan kasar zata kuma samun cigaba.

A karshe ina fatan sashen Hausa zasu dinga karanta ra'ayiyyikan da masu sauraro suke rubutawa a shafin zada zumunta na facebook a karshen karanta labaranku ko kuma a karshen shirye shiryanku, koda masu ma'ana daga ciki, domin wannan zai karawa masu sauraronku kwarin gwiwa da kuma sako gane masu bibiyar shafinku na facebook.

Ina maiku fatan alheri.

Kuhuta lafiya.

Wassalam,

ABDULKADIR IBRAHIM,

SHUGABAN KUNGIYAR,

GREAT WALL CRI LISTENERS' CLUB, KANO.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China