in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kada a yi miyau a duk inda aka ga dama
2013-05-08 16:42:34 cri

Ciwon tibi ya fi yaduwa a lokacin bazara. Masana sun tunatar da cewa, bin al'ada mai kyau a fannin kiwon lafiya ya zama tilas domin rigakafin ciwon tibi, musamman ma daina zubar da miyau duk inda aka ga dama.

Darektan cibiyar shawo kan cututtuka masu yaduwa ta jihar Xinjiang mai cin gashinkanta ta kasar Sin Mr. Gu Xiaoming ya bayyana mana cewa, ciwon tibi wani irin ciwo ne da ke yaduwa ta hanyoyin numfashi na jikunan mutane, kuma kwayoyin cutar tibi suna yaduwa sakamakon yin tari, yin atishawa, da tofar da miyau, Ta haka mutane za su kamu da wannan ciwo saboda sun yi numfashin feshin da ke kunshe da kwayoyin cutar tibi.

Kwayoyin cutar tibi su kan yi watanni 6 zuwa 8 a cikin miyau maras laima, wato busashe ke nan sa'an nan su kan yi kwanaki 8 zuwa 10 suna kasancewa cikin iska, saboda haka, hana zubar da miyau a duk inda aka ga dama, wani muhimmin mataki ne da ya dace a dauka domin rigakashin ciwon tibi.

Ban da wannan kuma, Mr. Gu Xiaoming yana ganin cewa, ana bukatar kara daukan matakan da aka ambata a gaba don shawo kan ciwon tibi.

Da farko dai, a mai da hankali kan mutanen da suke fama da ciwon tibi, a gano masu ciwon tun da wuri, a yi musu jiyya yadda ya kamata cikin hanzari. Mr. Gu ya yi bayanin cewa, rika yin tari da kuma tofar da miyau har tsawon kwanaki fiye da 3, ko kuma idan an gano jini a cikin miyaun da wani mutum ya yi, ana kyautata zaton ya kamu da wannan ciwo, kuma ya kamata ya je ya ga likita don neman shawara daga wajensu da yin bincike da kuma shawo kan wannan ciwo. Na biyu kuma shi ne, wajibi ne a dinga bude tagogi don shigar da iska mai tsabta kullun, da kuma motsa jiki, ta yadda mutane suna iya kara karfin garkuwar jikunansu. Na karshe kuma shi ne, kamata ya yi a yi allurar rigakafin ciwon tibi ga jarirai da kuma kananan yara cikin lokaci.(Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China