Dukka godiya ta tabbata ga Allah wanda ya bani daman rubuto muku wannan wasika. Tsira da aminci su tabbata ga Annabi Muhammadu SAW. Kamar kowane lokaci ya dace in jinjinama wannan gidan rediyon tare da maaikatansa akan jajircewa da tsage gaskiya kome dacinta. Ma'aikatanku ba su da kasala wajen shirya dadaddan shiraruwa da labaru da dimi-diminsu. Ina son ku kara tabbatar da cewa ni mai biye da shirye-shiryenku ne. Alal misali littafan Hausa, gaishe-gaishe da kuma amsoshin tambayoyi duk suna burgeni.
Naku Aiyu Abdullahi Dange, Karamar Hukumar Dange-Shuni, Jihar Sakkwaton Najeriya.