Bayan haka dafarko inason yin amfani da wannan dama gurin godewa sashen Hausa akan karanta wasikata danakayi akan gasar kacici-kacici jiya nagode. Haka kuma ina taya 'yan wasan kwallan kafa na Nijeriya kan lashe kofin kasashen Afirka na shekarar 2013 a kasar Afirka ta kudu.
Haka kuma inasanar jin dadin shirye-shiryanku dafarko ranar 5/2/13 na Sin da Afirka wanda Malam Bako ya tattauna da Alhaji Mustapha Muhammad dan kasuwa daga Nijeriya wanda yake gudanar da harkokin kasuwancinsa a kasar Sin. Lallai bayanansa ya kuma tabbatar da karamcin mutanen kasar Sin da baki masu zuwa kuma yanuna lallai kasar Sin itace zata zama shugabar kasashe anan gaba, kuma ni kaina ya kuma bani sha'awar yin kasuwanci akasar sin, domin dukda ni ma'aikacine yanzu innasami dama anan gaba zanyi wannan harka.
Sannan a ranar 6/2/13 shirinku na gani ya kori ya tattauna akan mahimmin abu wato kurbacewar muhalli da yadda za'a shawo kan matsalar dagolan masana'antu, gurbatacciyar iska, lallai abin da yafaru a birning Beijing ya kuma tabbatar da yadda ya kamata a maida da hankali akan wannan barbar matsala. Wannan shiri ya ilimantar da kowa a 'yan kungiya.
A karshe nake muku fatan alheri.
Wassalam,
Abdulkadir Ibrahim
Great Wall CRI Listeners Club. Kano.