Wasu mutane su kan ci kwai guda 5 ko 6 a ko wace rana, har ma wasu matan da suka haihu su kan ci kwai guda 10 zuwa 15 a rana. Suna tsammanin cewa tun da kwai na kunshe da abubuwa masu gina jiki, saboda haka cinsa da yawa na iya taimaka musu wajen samun koshin lafiya. Amma, a hakika dai ba haka ba.
Da farko, akwai sinadarin cholesterol da yawa a cikin kwai, idan mutum ya ci kwai da yawa, to zai kara yawan sidanarin a jinin jikinsa , hakan zai iya sa mutum ya kamu da cututtukan da ke da nasaba da zuciya da kwakwalwa.
Na biyu, cin kwai da yawa zai sa mutum ya samu abubuwa masu gina jiki da yawa har su wuce yawan abubuwan da mutum ke bukata, ta yadda za su taru a jikin mutum,su kuma sa mutum ya yi kiba.
Bayan haka kuma, cin kwai da yawa zai haddasa rashin daidaito tsakanin abubuwa masu gina jiki da ke jikin mutum, ta yadda zai iya kawo illa ga koshin lafiya. Abubuwan da mu kan ci na yau da kullum sun hada da abinci iri daban daban, kuma kamata ya yi su samar da sinadarai masu gina jiki da yawa, wadanda ke iya samun daidaito a jikin mutum, wannan ne zai sa mutum ya samu koshin lafiya.
Duk wani irin abincin ba ya kunshe da dukkan abubuwa masu gina jiki da mutum ke bukata. Idan an dauki lokaci mai tsawo ana cin abinci iri daya,wannan zai sa wasu sinadarai masu gina jiki da ke jikin mutum su yi yawa, amma a sa'I daya kuma jikin mutum zai rasa wasu sinadaran da yake bukata. Idan mutum ya ci kwai da yawa, to ko shakka babu sauran abubuwan da ya ci za su ragu, hakan zai sa a samu rashin daidaito tsakanin abubuwa masu gina jiki a jikin mutum, ta yadda rashin wasu abubuwa masu gina jiki cikin dogon lokaci zai haddasawa mutum wasu cututtuka.
Kazalika cin kwai da yawa na iya kawo illa ga hanta da koda. Idan aka ci kwai 1 zuwa 2 a rana, za a samu isasshun Sinadaran Amino acid irin 8 da jikin mutum ke bukata. Idan kuma aka ci kwai da yawa, to wasu dagwalon abubuwan da aka samu daga sinadarin da ke gina jiki za su fito daga jikin mutum ta koda, hakan zai iya kawo illa ga koda.
To kwai nawa ne ya kamata a ci a rana? Kwararru sun ba da shawara cewa, kamata ya yi tsofaffi su ci kwai 1 zuwa 2 a ko wace rana, matasa su ci kwai 2 a rana, ga wadanda ke aikin karfi kuwa, ya fi kyau su ci kwai 2 zuwa 3 a ko wace rana. Kana yara suna iya cin kwai 2 zuwa 3 a rana ta yadda za su girma cikin sauri. Mata masu juna biyu, da matan da suka haihu, da mutanen da aka yiwa tiyata suna iya cin kwai 3 zuwa 4 a rana, amma kada a wuce wannan adadi.(Bilkisu)