A.B.U. Teaching Hospital Zaria
Kaduna State Nigeria.
Zuwa ga Sashin Hausa,
Bayan gaisuwa da fatan alkhairi, ina ma farincikin sanardaku cewa na sami sakon da kuka aiko mini na Mujallarku ta Zumunta dakuma takardar gasar kacici kacici. Nagode sosai, saidai takardar ta sameni a latti sosai. Domin ban sami sakon ba sai january 2013.
Amma duk da haka a matsayina na mai saurarenku kimanin shekaru ashirin, kuma mai lura da al amurab yau dakullum zance wani abu.
"Hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka a idona" wani babban al amarine. Tsawon shekaru masu yawa Afirki tana cikin baqin talauci da yunwa da cututtuka dakuma yaqe yaqe ! Kasancewar kasashen Afirka a karkashin turawan mulkin mallaka ya qara habaka wadanna lamura... Allah ya albarkaci Afirka da yawan jama'a dakuma albarkatun kasa. Wadannan jama'a sunada kwazo da hazaka sosai, saidai qarancin Ilimi yana mayar dasu baya. Sannan kuma Afirka bata iya sarrafa ma'adananta da albarkatun noma yadd yakamata saboda qarancin fasaha da ilimi... Hakanan kuma mutanen Afirka basa iya sayen kayayyaki daga kasashen turai saboda tsada.
Itakuma Qasar Sin tanada matuqar ilimi, da basirar sarrafa kayayyaki dakuma ma'adanai. Sannan kuma qasar Sin tana bukatar inda zata sayarda kayayyakinta da ta sarrafa. Kuma kayan Sin sunada sauqi da dadewa wajen amfani.
To saboda wadannan dalilai yasa nake ganin Sin tana bukatar Afirka hakama Afirka tana bukatar Sin. Kamar bani gishiri in baka manda ne. Saidai Afirka zatafi amfana domin Sin tanada matuqar qarfin tattalin arziki.
Ina muku fatan alkhairi
Muhammad Aminu Idris