in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Muhimmiyar Sanarwa
2013-01-17 15:37:56 cri
Masu sauraro:

    Bayan dubun gaisuwa mai tarin yawa tare da fatan alheri da kuma fatan kuna cikin koshin lafiya kamar yadda muke a nan birnin Beijing, babban birnin kasar Sin.

    Muna farin cikin sanar da ku cewa, daga ran 1 ga watan Janairu na shekarar 2013, za mu fara wata gasar rubuce-rubuce mai taken "Ni da sashen Hausa na CRI cikin shekaru 50 da suka gabata" domin murnar cika shekaru 50 da kafa sashen Hausa na gidan rediyon kasar Sin CRI. Kuna iya rubuta dogon bayani ko wani zane da kuka zana dangane da haka ku aiko mana kafin ranar 31 ga watan Maris na shekarar 2013. Kamar yadda muka yi muku alkawari, za mu ba da kyaututtuka masu daraja ga wadanda suka rubuta bayani mai gamsarwa. Kuma za mu gayyaci wanda ya samu nasara ta musamman a gasar domin kawo ziyara a nan kasar Sin tare da halartar bikin murnar kafa sashen Hausa. Muna fatan za ku sami maki mai gamsarwa a cikin wannan gasa.

    Haza Wassalam

                                                                               Daga Sashen Hausa Na Rediyon kasar Sin

                                                                                                           1/1/2013

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China