A kan iyakar kasar Sin da Kyrgyzstan, a kafar dutsen Tian Shan, akwai wani karamar gunduma da ake kira "Aheqi", inda aka haifi Yusuf Mamay,wanda ya iya rera wakar da ake kira Manasi gaba daya, shi ma yana da shekaru 95 a duniya.
Gundumar Aheqi na karkashin jagorancin yankin Kizilsu Qirghiz na jihar Xinjing ta Uighur mai cin gashin kanta, wanda ke da yawan mutane dubu 50. Yawancinsu 'yan kabilar Kizilsu Qirghiz, da kuma akwai 'yan kabilar Han, Uighur da Hui da sauransu.
Wakar da ake kira Manasi ta sami asali daga gundumar Aheqi. Ko wata makaranta na da kos koyar da ilmin rera Manasi a gundumar. Ban da wannan kuma, a ko wace shekara, za a yi bikin rera Manasi.
Yusuf Mamay shi ne mutumin mafi muhimmanci ga Aheqi har ma ga dukkan jihar Xinjiang. Mutane da dama daga gida ko waje su zo wannan wuri ne domin yin hira da shi. Hakazalika, wasu manyan jami'an kasar Kyrgyzstan su kan kai ziyara a wurinsa domin gai da shi da sunbuci hannunsa, ciki har da mataimakin shugaban, ministan al'adu da sauransu. Ban da wannan kuma, a nan birnin Beijing, shugabannin kasar Sin sun yi hira da shi, har sun yaba masa cewa, shi daya daga cikin wasu muhimman mutane ne a kasar Sin.