in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ziyartar birnin Kashi
2012-08-15 20:50:29 cri

An ce, idan aka isa birnin Kashi, kamata ya yi a ziyarci kabarin marubucin littafin "Alheri da hikima" Yusuf Hays Hajip. Ni ma, lokacin ina dan karami, na kan karanta wannan littafi, sabo da haka, da na samu ji labari cewa, zan ziyarci kabarin wannan marubuci, na yi farin ciki sosai.

Kabarin Yusuf yana cibiyar birnin Kashi, kuma lokacin da na je sai na tuna da makabartun kasar Turkiyya, bayan da na isa wajen sai na ga mutum-mutumi na marubucin da yake rike da littafin "Alheri da hikima", sannan kuma na ga wani dandali, inda a dandalin ne kabarinsa kawai kewaye kuma rubuta da wasu jimlolin da ke cikin littafin, na karanta wadannan jimloli wadanda suka yi kama da harshen Turkiyya, kuma ina kokari in fahimci ma'anarsu.

A karni na 11, aka haifi Yusuf Hays Hajip a makabartan da ke birnin Kashi, ake binne shi shekarar 1077 bayan rasuwarsa. Daga shekarar 1069 zuwa shekarar 1070 ne kuma, ya rubuta wannan littafi na "Alheri da hikima".

Shi dai, wannan littafi ya kunshe bayani guda 85, wanda Yusuf ya rubuta shi cikin watanni 18 kacal.

Bayan da aka kafa jamhuriyar jama'ar kasar Sin, aka fara nazarin wannan littafi, kuma a shekarar 1979, an fara dab'in littafin da harshen Sinanci, a shekarar 1984, aka gurza irin littafi da harshen Uyghur. Sannan kuma a shekarar 1986 da shekarar 1989, an shirya taron kara wa juna sani game da wannan littafi tare kuma da kafa kwamintin nazarin littafin.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China