Na ji an ce, Sinawa su kan ce, abinci yana goban kome. Don haka, Sinawa sun dora muhimmanci sosai kan cin abinci. A wannan karo da na kai ziyara jihar Xinjiang, abinci iri 3 da suka fi jawo hankalina su ne kindirmo, burodi da kuma taliya.
Kindirmo na jihar Xinjiang ya yi kama da na kasarmu, yana da dadin sha. Yayin da nake birnin Beijing, na taba sayan kindirmo, amma ba na son shi. Kindirmon Beijing yana da yauki, na jihar Xinjiang ya fi dadi. Burodi na Xinjiang da na kasarmu suna da bambanci. Akwai babban burodi da karamin burodi a Xinjiang, kana suna da tauri. Amma burodi na kasar Syria yana da taushi, mu kan ci shi tare da nama da kayan lambu. Ba na son cin taliya ta Xinjiang, a kan ci irin wannan taliya tare da kwai da tumatir, kana a kan ji amo kadan yayin da ake cin taliyar, na yi mamaki sosai.