in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masallacin Atigar
2012-08-15 20:50:29 cri

Mun kai ziyara masallacin Atigar mai tarihi dake birnin Kashi na jihar Xinjiang a ranar 19 ga watan Yuni. Babban dandalin taruwar jama'a dake tsakiyar birnin yana wajen wannan masallaci ne, amma duk da haka shiru ka ke ji a cikin masallacin.

A kofar masallacin, akwai wani daki dake da wata fitila da aka rataya mai sifar fure inda wasu tattabara suke rayuwa. Kana akwai wata farfajiya a cikin masallacin, a kudu da arewa da farfajiyar akwai wasu dakuna. An ce, a wannan farfajiya ce liman yake karanta Alkur'ani da kuma bayar da darasi ga dalibai. Akwai kuma wasu kananan tabki guda biyu a cikin farfajiyar, a kewayensu an shuka nau'o'in itatuwa daban daban. Akwai wani babban yankin da ake yin salla a cikin masallacin, kuma an raba wannan daki zuwa sassa biyu. A cikin daya daga cikinsu, akwai ginshikai masu launin kore guda 140.

An ce, a kowace juma'a, mutane fiye da dubu shida n eke zuwa wannan masallaci mai shekaru fiye da 500 don yin salla. Kuma idan akwai wasu bukukuwa kamar sallar Lahiya da na Azumi, yawan musulmai da suke zuwa masallacin zai kai fiye da dubu 20.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China