in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakokin Gargajiya na Aites na kabilar Kazak a jihar Xinjiang
2012-08-15 15:29:33 cri






Kabilar Kazak dake zaune a jihar Xinjiang ta kasar Sin, kabila ce mai dadadden tarihi. A cikin kalmar "Aken Aites", "Aken" suna ne da aka lakabawa mawaka makiyaya na wannan kabila, kuma "Aites" na nufin muhawara a cikin harshen Kazak, wanda ya kasance wata hanya da 'yan kabilar su kan bi wajen rera waka. A yayin bukukuwa daban-daban na 'yan kabilar Kazak, ana iya ganin mawakan "Aken" suna zaune a kasa, inda maza da mata ke rera ma juna waka cikin halin annashuwa. To, idan 'yan kabilar Kazak sun ji amon wakokin, za su fito daga gidajensu don more wannan gagarumin biki tare.

Wani dan kabilar Kazak wanda ya zo daga yankin Changji na kabilar Hui mai zaman kansa na jihar Xinjiang, Murat ya gayawa wakilinmu cewa, dukkan 'yan kabilar Kazak na kaunar wakokin Aites, ko yanayi mai zafin gaske ko ruwan sama kamar da bakin kwarya, ba za su hana 'yan kabilar su taru don rera waka ba. Murat ya ce:

"Wakokin Aites ginshiki ne na zaman rayuwar 'yan kabilar Kazak, wadanda ke samar da zaman alheri da jin dadi ga mutanenmu. Ana iya cewa, babu wani dan kabilar Kazak da ba ya son Aites."

A wajen gasar rera wakokin Aites, mawaka su kan rera wakokin da suka shafi fannoni daban-daban, ciki har da tarihi, zaman rayuwar al'umma addini, siyasa, labarin kasa da sauransu. A wasu lokuta kuma, mawaka su kan rera wakoki ba dare ba rana don samun nasara a gasar. Don haka, kamata yayi mawaka 'yan kabilar Kazak su yi shiri sosai kafin su halarci irin wannan gasa.

Wata mawakiya 'yar kabilar Kazak mai suna Aysham Gul ta bayyana cewa:

"Rera wakokin Aites na bukatar mawakan Aken su nakalci ilimomi a fannoni da dama. A wannan zamanin da muke ciki, baya ga ilimomin gargajiya, ya zama dole mu karanta littattafai na zamani don samun ilimi, ta yadda za mu samu damar cin nasarar gasar rera wakoki."

Berik Tolepbergen, malami ne dake koyar da fasahohin amfani da kayan kida na Dombra a makarantar Yili dake jihar Xinjiang. Ya gayawa wakilinmu cewa, 'yan kabilar Kazak su kan ce, mawakan Aken su ne tsuntsaye dake iya rera wakoki masu dadi a duniya, kuma makada kayan kida na Dombra su ne tamkar dokin asbin. Duk inda mawaka 'yan kabilar Kazak su kan je, ba za su manta da Dombra ba.

Berik Tolepbergen ya bayyana cewa:

"Mu 'yan kabilar Kazak, makiyaya ne dake zaune a yankunan ciyayi. Mu kan mayar da kanmu tamkar shahon dake yin shawagi a sararin samaniya, sa'an nan kayan kida na Dombra gami da amon kida sun kasance fikafikai biyu na 'yan kabilarmu. Ba za'a iya raba mawakan kabilar Kazak da Dombra ba, a'a ba zai yiwu ba."

Akasarin 'yan kabilar Kazak su kan shafe duk tsawon rayuwarsu suna zaune a yankunan ciyayi masu fadi, abun da ya jawo musu cikas wajen samun ilimomi na zamani. Don haka wasu mawakan Aken masu iya rubuta wakoki su kan yi tattaki zuwa wurare daban-daban, su rubuta wakoki bisa abun da suke gani da tunani a kai, hakan ya sa aka bullo da wani nau'in salon fasaha na kabilar Kazak, wato Aken Aites, kuma ta hanyar rera wakoki ne 'yan kabilar Kazak suka gaji nagartattun al'adun gargajiyarsu zuriya bayan zuriya.

A nasa bangaren, wani babban jami'i mai kula da harkokin kare al'adun gargajiya da aka gada daga kaka da kakanni na jihar Xinjiang Mista Ma Yingsheng ya bayyana cewa:

"Yayin da suke rera wakokin gargajiya, mawakan Aken su kan gabatar da abubuwa masu muhimmanci ga jama'a, ciki har da tarihi, wasu muhimman al'amuran da suka wakana, labarai da dumi-duminsu da sauran makamanta. 'Yan kabilar Kazak su kan gaji muhimman dokoki da ka'idoji daga kaka da kakanninsu ta wannan hanya. Don haka muna iya cewa, wakokin Aites na taka rawar a-zo-a-gani a fannonin gadar al'adun gargajiya, nishadantar da jama'a da dai sauransu."

A watan Mayun shekara ta 2006, an sanya wakokin Aites na kabilar Kazak a cikin takardar jerin sunayen al'adun gargajiya da aka gada daga kaka da kakanni na kasar Sin, abun da ya taimaka sosai wajen kiyaye irin wannan al'adar gargajiya daga dukkan fannoni. Mista Ma Yingsheng ya gayawa wakilinmu cewa, domin kara baiwa mawakan Aken kwarin-gwiwar su halarci gasar rera wakokin gargajiya na Aites, da kuma habaka muhimmiyar rawar da wakokin ke takawa, hukumar jihar Xinjiang ta bada shawarar shirya gasar rera wakokin Aites sau daya a kowace shekara a kowane birnin jihar.

Mista Ma ya nuna cewa:

"Wannan tsari, wato shirya gasar rera wakokin Aites sau daya a kowace shekara, na samar da wani kyakkyawan zarafi da dandali ga matasa 'yan kabilar Kazak, wadanda ke kokarin koyon fasahohin rera wakokin gargajiya, don su yi mu'amala da cudanya tsakanin juna. Wannan taimakon da hukumar jihar Xinjiang ke samarwa na taimakawa sosai wajen kara bunkasa al'adun gargajiya na kabilar Kazak, abun da ya samu maraba kwarai da gaske daga al'ummar jihar."

Baya ga aikin gadar wakokin gargajiya na Aites da 'yan kabilar Kazak suke yi da kansu, gwamnatin jihar Xinjiang na nuna kwazo wajen yayata wannan al'adar gargajiya a cikin makarantu daban-daban. Shugaban cibiyar kiyaye al'adun gargajiya da aka gada daga kaka da kakanni ta yankin Yili na kabilar Kazak mai zaman kansa na jihar Xinjiang, Ohap Nurahmet, ya bayyana cewa, tun shekara ta 2004, a reshen kwalejin horas da malamai na yankin Yili dake Kuitun, aka kaddamar da wani kwas din koyar da fasahohin rera wakokin Aites. Ya zuwa yanzu, an horas da mutane sama da dari 3 a wannan yanki, wadanda ke da kwarewa a fannin rera wakokin Aites.

Ohap Nurahmet ya nuna cewa:

"Mawakan Aken, wani muhimmin sashi ne a cikin wakokin Aites. Idan muna so mu ci gaba da bunkasa wakokin Aites, kada mu manta da aikin horas da mawaka. Wannan kwas din da aka bude a reshen kwalejin horas da malamai na yankin Yili dake Kuitun na taimakawa kwarai da gaske wajen horas da mawakan Aken."

Daliban jami'o'i guda 32 daga kwalejin horas da malamai na Yili sun sanya tufafin gargajiya masu kyan-gani na kabilar Kazak, sun rera wakokin Aites tare da yin amfani da kayan kidan gargajiya na Dombra, a kokarin baiwa masu kallo damar morewa idanunsu gami da jin dadin wakokin gargajiya na kabilar Kazak wato Aites.

Darektar cibiyar kiyaye al'adun gargajiya da aka gada daga kaka da kakanni ta jihar Xinjiang Madam Li Jilian ta ce, wadannan mawakan Aken da suka kammala karatu a makaranta suna taka muhimmiyar rawa a fannin ci gaba da bunkasa wakokin Aites, bari mu ji abun da ta fada:

"Mu kan zabi mutanen dake da murya mai zaki da wadanda ke iya amfani da kayan kida don su koyi fasahohin rera wakokin gargajiya na Aites a makaranta, haka kuma ya zama dole su nakalci ilimomin zamani, hakan ya sa za mu horas da mawakan Aken masu kyau. Abu na daban shi ne, muna iya samar da wani kyakkyawan zarafi ga wadanda ke sha'awar wakokin Aites don su yi karatu, haka kuma muna iya samar musu da guraban ayyukan yi. Gaskiya wannan matakin da gwamnatin jihar Xinjiang ta dauka, wato kafa makaranta don koyar da fasahohin rera wakokin Aites na da ma'ana sosai."

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China