Matasa 'yan kabilar Uyghur 25 sun hadu, kuma sun kada kayan kidan Sataer, Eijieke, Kalun, Tanbuer, tare da busa, a sa'i daya kuma wasu daga cikinsu, suna rera wakar soyayya ta Muqram ta kabilarsu mai suna "Alifu da Sanaimu", shi dai salon wakar na da dadin ji, kuma wadannan matasa sun nuna himma da kwazo wajen rera waka, sabo da dukkansu sun kasance daliban da ke koyon ilmin fasahohi a sashen nazarin kide-kide na kwalejin koyon ilmin fasaha ta jihar Xinjiang dake kasar Sin, ga shi kuma shekarunsu sun kai kimanin 20, ga su suna da kyaun sura sosai, kana wakar Muqram da suka rera ita ma tana da halayye na musamman, abin da ya jawo hankalin jama'a sosai.
Akwai ni'imtattun wurare a Jihar Xinjiang da ke yankin arewa maso yammacin kasar Sin, kuma 'yan kabilar Uyghur da suke zaune a can suna kaunar zaman rayuwarsu, kuma suna kaunar albarkatun ruwan da suke da su cikin hamadar Sahara, a cikin shekaru dubu 2 da suka gabata, sakamakon karancin ruwan da suke da su, jihar Xinjiang ta zama tamkar wata gadar da ta hada da bambancin al'adu da yin mu'amala da sauran wurare, kuma an hada wayewar kai ta Girka, Sinawa da Larabawa a wannan wuri, wato inda kabilar Uyghur ke zaune, kuma an samu wani salon waka da ya hada da wakoki, raye-raye, da kide-kide, don haka aka lakaba wa irin wannan salon waka da suna Muqram, cikinsu, wakar Muqram da mutane 12 suka rera ta fi shahara, inda cikinsu ta kasu kashi 3, wato na farko kide-kide ne, na biyu kuma salon wakar da ke bayyana wa masu sauraro labari sai na uku kuma shi ne kide-kide da wake-wake a hade, sannan kuma ana bukatar awoyi sama da 20, idan aka son jin wakar Muqram da mutane 12 suka rera.
Masu sauraro, wakar da kuka saurara ta kasance wani zababben wakar da ke cikin wakar "Alifu da Sanaimu", kuma wannan wakar ta bayyana mana wani labarin soyayya, inda wani saurari mai suna Alifu da wata budurwa mai suna Sanaimu, suka shaku da juna, har daga karshe dai, suka yi aure, kuma wannan labari ya samu karbuwa a cikin dukkan unguwannin kabilar Uyghur, ana rera wannan waka tun daga zuriya bayan zuriya, kuma dan wasan kwaikwayo mafi farin jini na kasar Sin sannan dan wasan fasahar rera wakokin Muqram na kabilar Uyghur Osman Amat ya yi mana takaitaccen bayani game da wannan labari na "Alifu da Sanaimu", ya ce, "A lokacin da, wani sarki mai suna Abbas da hakiminsa mai suna Hasan sun fita waje don yin farauta, sai suka gamu da wata akuya mai juna biyu, sabo da tausayinsu, ba su son yanka ta ba, don haka, wadannan mutane biyu sai suka tsaida anniyar hada aure tsakanin yaransu, daga bisani sai Hasan ya rasu, kuma dansa Alifu da diyar sarkin Sanaimu da suka girma, sai kuma suka shaku da juna, amma kuma sabon hakimin sarki yana son batan wannan soyayya, sai ya zuga dansa kuma dogari Abdulshat da ya bata wannan kauna ta Alifu ta hanyar kulla makirci ga Alifu, ya kuma yada jita-jita a gidan sarki, inda bayan da sarkin ya ji wadannan jita-jita, ya kori Alifu da duk iyayensa zuwa wani garin daban, sabo da haka, Sanaimu ta yi bakin ciki sosai, har ma ta fara rashin lafiya, kamar za ta mutu. Haka kuma, shi ma Alifu ya gamu da wahalhalu da dama, a karshe dai, a karkashin taimako daga manoma, ya sake shiga cikin gidan sarki, yayin da ake gina lambun shan iska a gidan sarki, ya kashe Abdulshat, kuma ya fallasa makircin da ya kulla masa, a wannan lokaci kuma, Sarki ya yi da-na-sani, kuma ya tuba, ya nemi shi gafara sannan ya amince aka yi bikin soyayya tsakanin Alifu da Sanaimu."
Osman Amat ya fada wa wakilinmu cewa, labarin soyayya na Alifu da Sanaimu ya faro ne daga karni na 10, kuma mai tsara wakoki na kabilar Uyghur Yusuf Ali ya tsara wannan waka daga cikin wani labari, labarin dake sosa zuciya sannan kuma salon wakar sun dace da juna, kana wakar ya samu karbuwa a cikin al'ummar kabilar Uyghur.
Tsohon malami dan kabilar Uyghur, Samsack Amat mai shekaru 85 a duniya, yana zaune ne a kauyen Bostan da ke gundumar Kalatale a birnin Akesu dake jihar Xinjiang mai cin gashin kanta a kasar Sin. A shekarar 1940, a matsayinsa na wani makiyaya, yayin da yake kiwon awaki, a lokacin ya fara koyon wakar Muqram don kawar da kewa, sabo da bai yi makaranta ba, amma ya haddace salon wakar Muqram. A kwana tashi, ya zuwa yanzu, shekaru 72 ke nan, amma wannan dattijo na ya ci gaba da bayyana mana labarin soyayya tsakanin Alifu da Sanaimu. Ya ce, a cikin wakar Muqram da mutane 12 suka rera, akwai labarin soyayya da irin wahalhalun da suka gamu da su, sannan kuma suna jin dadinsu, yayin da ya yi kokarin bayyana mana wannan labari, wannan dattijo ya fara buga ganga da kansa, kuma a take ya jagoranci magoyon bayansa don rera wannan waka, sabo da bayyana mana irin bakin ciki na Alifu, yayin da aka kai shi garin daban da tunaninsa game da masoyarsa. Masu sauraro, bari mu ji wakar, "Masoyiyata, ina kike? Abin bakin ciki ne, an sa mana ankwa, kuma idan ban ganki ba, zan mutu, 'yan fashi marasa imani, suka yi yunkurin kashe ni! Masoyiyata, idan ban ganki ba, zan mutu."
Domin bayyana irin kaunar da ke tsakanin wannan saurayi da budurwarsa, dan wasan fasahar Muqram na kabilar Uyghur Osman Amat ya rera mana wani bangare daga cikin wakar da Alifu ya rera don bayyana kaunarsa ga Sanaimu. Masu sauraro, bari mu ji wakar, "Surarki na da kyau, kuma idan ki kalle ni, zan ji dadi, ban iya mantawa da ke, kuma na shaku da ke."
A karshe dai, Alifu da Sanaimu, sun sake haduwa, yayin da ake bikin aure, wakoki masu dadin ji, da salon wakar sun kawar da bakin cikinsu, kuma sun bayyana alfaharinsu da tunaninsu game da makomarsu. Masu sauraro, yanzu bari mu ji wakar.
Direktan sashen nazarin wakar Muqram na cibiyar nazarin fasahohin jihar Xinjiang Mijisiyunus ya fada wa wakilinmu cewa, wannan salon wakar mai dadin ji kuma ya bayyana mana karshen labarin soyayya da ke tsakaninsu, wato sun shaku da juna kwarai, ya ce,"wannan salon wakar Muqram ya bayyana yanayin da ake ciki yayin da Alifu da Sanaimu suke bikin aure, kuma sarkin ya amince da aurensu, sabo da haka, salon wakar na da annashuwa, kuma wakar na da dadin ji sosai."
Masu sauraro, yayin da aka ji wannan labarin soyayya, za a tuna da wani karin magana na kabilar Uyghur, wanda ke cewa, idan mutum ya ketare hamadar Sahara, zai isa wurin da ke da albarkatun ruwa, kuma labarin soyayya shi ma haka yake, bayan da Alifu da Sanaimu suka sha wahalhalu da dama, sun samu sakamako mai gamsarwa. Ya zuwa yanzu, salon wakar Muqram mai sosa zuciyar mutane tare da labarin soyayya na kabilar Uyghur, ba ma kawai sun samu karbuwa a kabilar Uyghur ba, hatta ma a shekarar 1980, an dauki hoton bidiyo, sannan wannan waka ya samu karbuwa a gida da waje. Bugu da kari, shahararren mawaki nan dan kasar Sin Dao Lang shi me ya yi amfani da wannan labarin soyayya, don tsara wata wakar mai suna "Alifu da Sanaimu" mai tagomashi , Masu sauraro, yanzu bari mu ji wakar. "Tun lokacin da muke yara, mun hadu a dutsen Tianshan, kuma da ma, mun kasance mutane masu sa'a, Sanaimu, ke sarauniyar mata ce, kuma ni ne Alifu ina so in zama abokinka na soyayya."
A shekarar 2005, kungiyar kula da harkokin kimiyya, ilmi da al'adu ta M.D.D UNESCO ta sanar cewa, za a mayar da wasan fasahar Muqram ta kabilar Uyghur ta jihar Xinjiang a kasar Sin a matsayin abubuwan da aka gada daga kaka da kakanni ta baka. Haka kuma, a shekarar 2010, jihar Xinjiang ta fitar da wata ka'idar don kare fasahar Muqram ta kabilar Uyghur, kuma wannan ka'ida ta zama ka'ida ta farko da aka aiwatar da ita a wata jihar da ke kasar Sin don kare abubuwan da aka gada daga kaka da kakani. Shugabar cibiyar nazarin fasaha ta jihar Xinjiang kuma direktar cibiyar nazarin al'adun da aka gada daga kaka da kakanni, Li Jilian ta ce, salon wakar Muqram ya kasance wani salon waka da za ta bayyana mana zaman rayuwar al'umma da yanayin da ake ciki a jihar Xinjiang ta baka, sabo da haka, an mai da hankali sosai wajen ba da kariya ga fasahar Muqram da nuna goyon baya ga mutanen da suke iya wannan fasaha, Madam Li ta ce, "Dan wasan fasahar Muqram da ya gaji fasaha daga kaka da kakanni ya kan samu taimakon kudi da yawansu ya kai kudin Sin Yuan dubu 10 a ko wace shekara, kuma gwamnatin jihar Xinjiang ita ma za ta ba da kudin kyauta wato bonas nata da yawansu ya kai Yuan 3600 ga ko wane dan fasaha a ko wace shekara, haka kuma ko wane 'yan wasan fasahar zai iya samu kudin taimako da yawansa ya kai Yuan 200 zuwa 500 daga gwamnatocin gudummomi ko matakai daban daban a ko wace shekara, kuma za a yi amfani da wadannan kudade don sa kaimi ga wadannan 'yan fasahohi don su raya fasahar Muqram."
Yanzu haka, a jihar Xinjiang akwai wani karin magana da ake cewa, idan wani dan kabilar Uyghur ya iya magana, ya iya waka, idan ya iya tafiya, to, ya iya rawa. Don haka yanzu, a ko wace gunduma a ko wane kauye, akwai kungiyar masu rera wakokin Muqram, ko wane dan kabilar Uyghur ya iya rera waka da kida, haka kuma, suna iya yin rawar Muqram, kuma yanzu, fasahar Muqram ta zama wani muhimmin bangare da ke cikin zaman rayuwarsu, sannan kuma Muqram ta zama wani babban jigo ne da ke cikin rayuwarsu.