in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakar "Janggar ta kabilar Mongoliya" da aka dade ana rerawa
2012-08-15 14:02:15 cri






Jama'a masu karatu, yanzu sai ku karanta wani sabon bayani mai lakabi "wakar Janggar ta kabilar Mongoliya" na jerin shirye-shirye game da al'adar jihar Xinjiang ta kasar Sin.

Jama'a masu karatu, Jianger, wani nagartaccen sarki ne Jarumi da ya yi suna a tarihin al'ummar Mongoliya. A lokacin da yake sarautar yankin Mongoliya yau fiye da shekaru dubu 1, ya yi yake-yake da dama domin fadada fadin kasarsa ta Mongoliya da kuma kawo kwanciyar hankali da alheri ga jama'arsa ta Mongoliya. Sabo da haka, a cikin shekaru fiye da dubu 1 da suka gabata, al'ummomin Mongoliya su kan rera wakokin yaba mashi, har ma ya kai ga an rubuta wata doguwar waka mai suna "Janggar".

Bisa tatsuniyoyin da aka yada, an ce, a lokacin da Janggar yake karami, iyayensa sun mutu, ya girma a wani maraya. Amma a yayin da ya kai shekaru 3 na haihuwa, ya lashe dodunan da suka kai farmaki kan filayen ciyayi inda 'yan Mongoliya suke zaune, har ma ya lashe sarkuna 42 wadanda suka yi mulki a yankuna 42, kuma ya kafa kasar Bumba a kokarin kawo alheri ga 'yan kabilar Mongoliya. Amma yaya hakikanin halayen marigayi sarki Janggar?

Kamar yadda aka bayyana a cikin wakar: sarki Janggar yana da karfi da hikima da Allah ya ba shi, kuma akwai karfin da dodannin (dragon) bakwai suka ba shi a kafadarsa, har ma yana da jikin dake hade da karfin giwaye saba'in. Sarki Janggar yana da kyaun gani, kuma ya fi kwarewa a cikin jarumai wadanda suka kware wajen hawan doki. Ya kasance kamar wani jarumin saurayi da shekarunsa na haihuwa ba zai wuce 25 ba har abada a cikin zuciyar jama'ar Mongoliya, a cewar wakar "Janggar".

A cikin wannan waka, an bayyana Janggar kamar wani dodo, Shin ko akwai wani sarki Janggar da ya kasance a tarihin al'ummomin Mongoliya? Wa ya rubuta wannan doguwar waka "Janggar"?

Har yanzu ana yada labaru a tsakanin al'ummar Mongoliya game da yadda aka tsara, yada, gyara, bunkasa da kuma tabbatar da wakar "Janggar" a karshe a tarihi. Game da wurin da aka soma rera wannan wakar "Janggar", masana suna tsammani cewa, akwai wurare uku da al'ummomin Mongoliya daban daban suka zauna. Wadannan wurare uku kuwa su ne: Khalimag na yankin da kogin Volga ke shafar na kasar Rasha, sannan wani daban shi ne yankin da kasar Mongoliya ta yanzu ke ciki, na ukun kuma shi ne yankin Tsingger. Bayan da masana suka kwatanta sunayen wuraren da aka ambata a cikin wakar "Janggar", sun yi tsammani cewa, maganar wai wakar "Janggar" ta fito daga yankin Tsingger na jihar Xinjiang ta fi daidai, amma har yanzu babu hakikanan abubuwan tarihi na shaidar kasancewar sarki Janggar da kasar Bumba da ya kafa. Shehun malami Jia Mucha na jami'ar Xinjiang wanda ya kware wajen nazarin wakar "Janggar" yana ganin cewa, Janggar a hakika dai ba wani mutum ba ne, kawai dai alamar ne dake wakiltar jaruman al'ummar Mongoliya, ciki har da sarki Chendjishan wadanda suke da niyyar shigar da al'ummar Mongoliya cikin muhimman al'ummomin duniya.

Shehun malami Jia Mucha ya ce, "Sunan Janggar ba harshen Mongoliya ba, harshen Persian ne daga waje. Ma'anar Janggar ita ce 'wanda ya mallaki duniya baki daya'. Sabo da haka, galibin masana suna tsammanin cewa, an fara rubuta da yada wakar Janggar ne a lokacin da jaruman al'ummar Mongoliya ke fitowa tun daga karni 12 zuwa karni 14 bisa abubuwan da jarumai, ciki har da sarki Chendjishan suka yi. Masanan kasar Rasha sun taba bayyana cewa, wakar 'Janggar' tarihi ne da aka rubuta tare da kalmomin ado da na kayatarwa a kokarin yaba jaruman al'ummar Mongoliya."

Ba ma kawai "Wakar Janggar" wata doguwar waka ce da yake yaduwa ta bakin al'ummar Mongoliya ta kasar Sin ba, ta kuma kasance tamkar wani littafi ne dake da daraja mai yin nazarin al'adar Mongoliya ta Xinjiang. Galibin abubuwan da ake yabawa a cikin wakar su ne muhimman al'amurra da jarumai da suka kasance a tarihi, kuma suna kunshe da tarihi, al'adu, zaman al'umma da dai sauransu na kabilar Mongoliya wadanda suke bayyana yadda al'ummar Mongoliya suke zama a doron duniya.

Jama'a masu karatu, mai yiyuwa ne za ku so tambayar wane ne ya bayar da gudummawa wajen tsara, kara abubuwa, gyara da kuma yada wannan doguwar wakar "Janggar"? To, bisa nazarin da aka yi dai, an gano cewa, mutane masu sha'awar wakar "Janggar", wato a kan kira su "Janggarci" cikin harshen Mongoliya. A cikin harshen Mongoliya, ma'anar "ci" ita ce, "wanda ya kware kan wani aiki". Don haka, ma'anar "Janggarci" ita ce wadanda suka kware kan rera da kuma yada wakar "Janggar" da bakinsu. Sabo da ana yada wakar "Janggar" ta bakin jama'a, ana bukatar suna da fasahar rera da kuma karfin haddace wakar. Amma yanzu ana kokarin neman ci gaban duk duniya bai daya, zaman al'ummar ma na hanzarta samun sauye-sauye, har ma fasahohin zamani na kawo tasiri sosai ga al'adu, wadannan sauye-sauye ke sa kokarin kare da kuma yada wakar "Janggar" ya fuskanci sabon kalubale iri iri. Yanzu dimbin nagartattun mutane masu rera da kuma yada wakar "Janggar" sun riga mu gidan gaskiya, kuma wadanda har yanzu suke raye sun tsufa matuka. Sabili da haka, yadda za a ci gaba da yada wakar "Janggar" da kare wadanda suka kware kan rera wakar ya zama wani muhimmin aiki a gaban gwamnatin kasar Sin.

A ran 20 ga watan Mayu na shekarar ta 2006, bisa amincewar gwamnatin kasar Sin, wakar "Janggar" ta shiga takardar sunayen abubuwan tarihi na al'adun da aka gada daga kakanni da kakanni ta kasar Sin. Sannan gwamnatoci a matakai daban daban na jihar Xinjiang sun dauki matakai daban daban a kokarin kara karfin kare wakar "Janggar". Mr. Ma Yingsheng, wani jami'in da ke aiki a sashen kare abubuwan tarihi na al'adun da aka gada daga kakanni da kakanni na hukumar al'adun jihar Xinjiang ya gaya wa wakilin CRI cewa, "Gwamnatinmu ta dauki matakai daban daban. Matakin farko shi ne, an shigar da wakar a cikin takardar sunayen abubuwan tarihi na al'adun da aka gada daga kakanni da kakanni domin tabbatar da darajarta. Sannan gwamnatoci a matakai daban daban sun kara kebe kudi kan aikin kare wakar, wato sun kebe wa wadanda suka kware kan rera wakar tallafin kudi, shirya kwas-kwas tare da makarantun boko domin koyar da kuma yada wakar. Kana sun kafa wani tsari na yada wakar, kamar shirya bukukuwa da gasannin rera wakar. Daga karshe dai, sun kafa hukuma ko gina cibiya na koyar da kuma nune-nunen hoton bidiyon wakar. A matsayin hukumar gwamnati dake kula da harkokin al'adu, abin da muka fi mai da hankali a kai shi ne horar da mutane wadanda suke da niyyar koyon rera da kuma yada wakar. A cikin dukkan matakan kare wakar, kare wadanda suka kware kan rera wakar ya fi muhimmanci."

Dattijo Shariniman, wani sannanen Janggarci ne a gundummar Hejing ta jihar Xinjiang. A watan Yuni na shekarar ta 2007, ma'aikatar al'adun kasar Sin ta zabe shi da ya zama wakilin mutane wadanda suka kware kan rera da kuma yada wakar Janggar, har ma ya shiga sahun nagartattun mutane 226 wadanda suka kware kan gadan abubuwan tarihi na al'adun da aka gada daga kakanni da kakanni.

An haifi Shariniman ne a wani gida, inda iyaye da kakanni-kakaninsa suka kware sosai kan rera wakar Janggar. Don haka, tun da yake karami, ya nuna sha'awa sosai kan rera wakar. Har yanzu yana iya rera babi 26 na wakar Janggar. Dattijo Shariniman ya dukufa ka'in da na'in wajen rera da kuma yada wakar Janggar, kuma yawan daliban da ya koyar sun kai 53, kuma guda 8 daga cikinsu sun zama Janggarci. Ba ma kawai dattijo Shariniman na koyar da dalibai da kansa ba, har ma yana koyar da fasahar rera wakar a makarantar midil ta hudu ta gundummar Hejing a kowane mako. Dattijo Shariniman ya ce, ko da yake ana fuskantar matsaloli iri iri wajen yada wakar Janggar, amma ruhun jarumi Janggar na sa masa kaimi wajen fama da su, har ya samu nasara. Dattijo Shariniman ya gaya wa wakilinmu cikin harshen Mongoliya cewa, "Ruhun Janggar shi ne za a tinkari matsaloli iri iri, amma ba za a ba da kai ba. Idan babu irin wannan ruhu, shi ke nan, ba za mu samu kome ba kwata kwata."

Jama'a masu karatu, a watan Satumba na shekarar 2007, an kafa sansanin koyon wakar Janggar a makarantar midil ta hudu ta gundumar Hejing ta jihar Xinjiang. Ya zuwa yanzu yawan daliban da suke koyon fasahar rera wakar ya kai su dari . Mr. Mandulai, wani dalibin dattijo Shariniman ne kuma shi ma ya bi sawun malaminsa yana koyar da fasahar rera wakar a wannan sansani. Bisa taimakawar Mandulai, yanzu dalibai 54 suna iya rera babi 1 ko babi 2 na wakar Janggar. Mandulai ya bayyana cikin harshen Mongoliya cewa, "suna kokari kwarai. Dalibai da yawa suna da sha'awar koyon fasahar rera wakar Janggar, kuma wasu daga cikinsu sun ce, suna son zama Janggarci bayan da suka girma. Don haka, a ganina, makomar yada wakar Janggar tana da haske."

A hakika dai, wakar Janggar ta zama wata doguwar wakar da ta yi suna a yankunan kabilar Mongliya da yawa a kai a kai sakamakon kaurar kabilar da kuma yake-yaken da aka yi a tsakanin al'ummar Mongoliya. Bisa abubuwan tarihin da aka samu, an shaida cewa, ko a kasar Sin, ko a kasar Rasha, ko a jamhuriyar Mongoliya, a duk inda al'ummar Mongoliya ke zaune, ana shirya bukukuwan rera wakar Janggar. Sakamakon haka, a kan ce, al'adun wata kabila, tabbas ne al'adu ne na duk duniya. Mr. Ma Yingsheng, wato jami'in hukumar al'adun jihar Xinjiang ya ce, an shigar da aikin kare da kuma gada wakar Janggar a cikin muhimmiyar ajandar yin hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa ta fuskar kare abubuwan tarihi na al'adun da aka gada daga kakanni da kakanni. Mr. Ma Yingsheng ya ce, "Nauyin da aka dora mana shi ne yada wakar Janggar ga sauran kasashen duniya. Yanzu muna kokarin shigar da wakar Janggar a cikin takardar abubuwan tarihi na al'adun da aka gada daga kakanni da kakanni na kasa da kasa. Kana muna kokarin yin hadin giwwa tare da jamhuriyar Mongoliya a kokarin bayar da gudummawa da taka rawa wajen kare wakar Janggar da sauran abubuwan tarihi dake bayyana al'adun al'ummar Mongoliya."

"Fada mai launin fata tana da kayatarwa da girma, doki mai launin ja shi ne doki Aranzhale wanda ke gudu cikin sauri, kana kasar Bumba kasa ce mai wadata." Ko da yake shekaru fiye da dubu 1 sun wuce, amma har yanzu ruhun jarumi Janggar ya zama jinin al'ummar Mongoliya. Tabbas ne al'ummar Mongoliya za su ci gaba da gadan wakar Janggar kamar yadda suka gaji ruhun jarumi Janggar.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China