Masu karatu, yau za mu gabatar muku shiri na 3 daga cikin shirye-shiryen musamman na 'Fahimtar jihar xinjiang,sanin al'adunta', wanda ke da taken 'Wakar tarihi ta kabilar Kirgiz mai taken Manas'. Watakila za ku yi tambaya cewa, mene ne wakar tarihi? Ko kuma mene ne abun da wakar ta bayyana? To, a shirin yau za mu ba ku amsa mai gamsarwa, sai ku bi mu.
Masu karatu, muryar da kuka ji dazu ta kasance yadda ake rera babi na farko na wakar Manas, wadda aka bayyana ta a matsayin 'kundin da ya hada ilmi a fannoni daban daban na al'ummar Kirgiz ta kasar Sin'. A shirinmu na yau, zan kai ku zuwa wurin da aka samu asalin wannan waka ne mai taken Manas, wato gudumar Akqi ta yankin Kirgiz dake jihar Xinjiang na kasar Sin, inda za mu saurari wakar Manas, kana za mu yi kokarin fahimtar asalin wakar da tarihinta.
Gundumar Akqi ta kasance a kan iyakar kasar Sin da kasar Kirgizstan. Da ka isa wurin, za ka ga ba shi da girma, kuma duwatsu na kewayensa. Sa'an nan da ka shiga cikin gundumar, za ka ji kamar kana shigowa cikin wani wurin da aka bayyana cikin tatsuniya, domin muhallin wurin yana da kyau ainun. Za ka ga kankara ta rufe koluluwan duwatsu dake wuri mai nisa, sa'an nan a sararin samaniya mai launin shudi za ka ga gajimaren dake shawagi sannu a hankali. Idan ka karkata idanunka zuwa ga babban filin ciyayi, za ka ga shanu da awaki suna yawo suna cin ciyawa, wannan muhalli ya kan sa hankalin mutum ya kwanta ya kuma fara jin dadi. To, 'yan kabilar Kirgiz dai sun fara zama a kan filayen ciyayi tun kaka da kakaninsu, inda suke kiwon dabbobi, da zaman rayuwa, tare da kirkiro tatsuniyoyi da labaru masu dadin ji. Kana wakar Manas, wadda 'yan Kirgiz suke rerawa a cikin shekaru fiye da dubu daya da suka wuce don bayyana da tunanin tarihinsu, ta kunshi labari mafi dadin ji da 'yan Kirgiz suka kirkiro, kamar yadda aka bayyana a cikin wakar:
'kakaninmu sun ba mu wadannan labaran, yaya za mu iya dainawa a tsakiya, ba mu rera su tun daga farko har zuwa na karshe ba?...an yi sauyi da yawa a kan kasa, inda koguna sun shanye sun zama filaye marasa ciyayi, kana filaye sun zama tabki, sa'an nan tabki ya zama gonaki,…kome da kome na sauyawa, sai dai labari game da jarumi kamar zaki na Manas yana ta bazuwa har zuwa yanzu.'
'Kazamar fada da aka yi ta sanya manyan duwatsu girgiza, ruwan koguna ma sun daina gudana. Kurar da aka tayar a filin daga ta boye mayaka a ciki, don haka rana ma ta yi dubu ta raya haskenta.'
Masu karatu, wannan babi daga cikin wakar Manas da kuka saurara ya bayyana yanayin yaki wanda ke tayar da hankalin mutum. Wakar Manas ta yaba wa jarumi mai suna Manas da zuriyoyinsa, wadanda suka jagoranci al'ummar 'yan kabilar Kirgiz wajen fama da abokan gaba da suka kai musu hari a tarihin a'ummar Kirgiz. Wannan waka, da tarihin da ta bayyana, suna karfafawa 'yan kabilar Kirgiz kwarin gwiwa, don haka su kan nuna himma da kwazo, da jarumtaka a kowane irin hali mai wuya. Ma iya cewa wannan tarihi ya tabbatar da kasancewar jaruntaka da karfin zuciya cikin tunanin jama'ar Kirgiz.
Jama'ar kabilar Kirgiz dake zama kan makeken filin ciyayi sun kasance mutane ne da suka kware kan fasahar kida, da kirkiro al'adu ta baki, don haka a kan ga yadda ake samun damar gadon al'adun kabilar da bazuwa da su ta bakin mutum. Wakar Manas ta zama wani fitaccen misali a wannan fanni ke nan, wadda ba ta da rubutaccen leben waka, balle ma rubutaccen bayani game da kidanta. Don haka wakar tana samun bazuwa ne ta baki da kunnuwan mutum kacokam. Zuriya da zuriyoyi, 'yan kabilar Kirgiz suna ta rera wannan waka. Muryarsu ta ratsa gajimare da ke saman yankin tsaunuka na Pamir, da ketare manyan filayen ciyayi da suke zama, wadda ta fara daga karni na 10, ta dade har zuwa yanzu. Wadannan mawaka da suke koyon fasahar rera Manas gami da baza ta suna da lakabi guda, wato Manaski.
Masu karatu, muryar da kuka ji ta kasance yadda wani shahararren Manaski, wato mawaki dake rera wakar Manas, mai suna Jusuf Mamayi, yake rera wakarsa ta Manas. A tsakanin al'ummar Kirgiz, idan ka ambaci sunan Jusuf Mamayi, sai ka ga kamar babu wanda bai san shi ba. Domin yana da wata fasaha mai burge mutane: ya iya rera wakar Manas tun daga farkonta har zuwa karshe, wacce bayanin dake cikinta idan an tsara shi cikin littafi zai kunshi layuka dubu 230! Don haka, ana ganin Jusuf Mamayi a matsayin wanda ya fi kwarewa wajen rera wata cikakkiyar wakar ta Manas, wannan ma ya sa ake kiransa 'Homeros dake rayuwa'. Wannan mutum mai suna Homeros mun san shi ne fitaccen mawaki da ya tsara wasu wakokin tarihi 2 masu tsayi wandanda kuma ke da muhimmanci a duniya, musamman ma ga tarihin Turawa, wato Iliad da Odyssey.
To, mu koma wajen bayanin da muke kan Jusuf Mamayi. Lokacin da wakilin CRI ya gan shi, ya ga wannan tsohon tamkar mutumin da a kan bayyana a cikin tatsoniyoyi wato wani tsoho mai farin geme, wanda za a iya ganin kirkinsa ta fuskarsa. Duk da cewa shekarunsa sun kusan kai 96 a duniya, amma ana iya ganin alamar basiri a cikin idanunsa. An ce, dattijon nan, tun lokacin da yake da shekaru 8 da haihuwa, ya fara koyon fasahar rera wakar Manas daga wajen wansa wanda ya girme shi da shekaru 22. Bayan da ya zama baligi, ya riga ya tike fasahar rera cikakkiyar wakar Manas bisa tunaninsa.
Yayin da 'yan kabilar Kirgiz suke tsananin kishin wakar tarihinsu ta Manas, suna girmama Manaski, wato mutane masu rera wakar. Wadannan mutane sun taka muhimmiyar rawa a kokarin tabbatar da bayyananniyar wakar Manas daga zuriya zuwa zuriya. Suna da fitacciyar kwarewa wajen rike abubuwa a zuciya. Kana a lokacin da suke rera waka, suna iya samar da wata murya mai dadin ji. Duk da cewa ba su amfani da kayan kida, amma su kan nuna himma sosai, da yawan yin amfani da fuskarsu wajen nuna abin da suke son bayyanawa. A wani lokaci suna rera waka da babbar murya, a wani daban kuma sai su kwantar da murya, tare da yin amfani da hannayensu don bayyana wasu abubuwa. Don haka, yayin da ake sauraron muryar Manaski, zai yi kamar ana kallon wani mashahurin wasan kwaiwayon ne na tarihi, abin da kan burge mutane sosai. Kusan dukkan Manaski kwararrru, yayin da suke magana kan tarihinsu wajen koyon fasahar rera wakar Manas, su kan bayyana cewa akwai wani mala'ika da ke koyar musu wannan fasaha a lokacin da suke barci. Suna da imanin cewa, wannan fasahar ta kasance wata alama ce da gunkinsu ya nuna musu.Wani Manaski mai suna Kurmanali ya bayyana kamar haka:
"Wakar Manas ita ce tarihi kuma ruhu na al'ummar mu. Tun da da da can, kakaninmu sun fara rera ta. Zuriyarmu su ma suna kokarin koyon fasahar rera ta. Don haka, ba mu ga wani abu mai wuya ba wajen rike wannan waka mai tsayi. Mun rike ta bisa koyarwa ta baki tsakanin zuriyoyi."
Kurmanali, wanda ya fara koyon wakar Manas tun yana da shekaru 10 a duniya, wanda kuma ya fara bin Jusuf Mamayi domin koyon fasahar rera wakar tun lokacin yana da shekaru 20 a duniya, yana da shekaru 69 a bana. Yayin da dattijo ya bude baki ya fara rera waka, masu sauraro za su iya ganin kishi mai tsanani da ya nuna wa wakar ta haryar alamun fuskarsa da muryarsa, abin da ya burge mutane sosai. Akwai Manaski da dama da suke iya rera waka ba dare ba rana, har ma su kan dade suna rera wa a tsawon kwanaki fiye da goma. Kurmanali ya kasance da ya daga cikinsu:
'Kafin na tsufa, a wani lokaci, na taba rera waka har tsawon sa'o'i 24 ba tare da tsayawa ba. Amma yanzu ba na da karfin jiki, iyakacina yanzu zan iya rera wakar na tsaron awa daya ne kawai.'
'Yar Kurmanali mai suna Goncagul ita ce mai rera Manas, kuma yawan shekarunta za ta kai 19 a bana. Jusuf Mamayi yana da dalibai 40, a cikinsu akwai masu rera Manas mata guda 4 kamar Goncagul. Yanzu dai, mata na kabilar Kirgiz sun iya gwada shirye-shirye a kan dandalin rera wakoki kamar maza, wadanda suka kasance muhimmiyar kungiya da ta rera Manas. Game da yadda suka san Manas, Goncagul ta ce,
"Tun daga lokacin da na kai shekaru 13, na koyi rera Manas daga mahaifina, kuma mahaifina ya nuna goyon baya sosai gare ni don zama wata Manaski. Ni wata daliba ce ta Jusuf Mamayi. Domin na koyi Manas daga mahaifina tun daga kuruciya, sabo da haka, kamar sauran masu rera Manas, babu wuya gare ni wajen koyar Manas."
Kamar yadda masu rera Manas suka rera, "hali yana canjawa, amma an gaji labaru daga kaka-kakanni." A halin yanzu, an samu babban canji a garin Akqi da aka haifi Manas, ana samun internet, wato yanar gizon sadarwa, sinima, telebijin a zaman rayuwar makiyaya a garin. Matasa ba su kan rera Manas lokacin da suke kiwo kamar lokacin da. Domin babban ci gaba kan kimiyya da fasaha da raya duniya bai daya, ana fuskantar kalubale wajen kiyaye Manas, abin al'adun gargajiya na tarihi da aka gada daga kakanni ba na kayayyaki ba. Wani mai yin nazari na cibiyar nazari kan Manas ta garin Akqi Abdu ya bayyana cewa,
"An gada Manas ta baki, babu rubuta. Sabo da haka, mun gaje shi ta hanyar baki. A kowace shekara, muna gudanar da bukukuwan rera Manas, kana an bullo da darasi na koyar Manas a makarantu. Gwamnatin yankin ta gudanar da ayyuka da dama don kiyaye da yada Manas."
Manas ita ce abu mafi muhimmanci na gwada fasahohin 'yan kabilar Kirgiz, don haka kiyaye Manas yana da muhimmanci sosai. A ranar 20 ga watan Mayu na shekarar 2006, an shigar da Manas a cikin jerin sunayen abubuwan al'adun gargajiya na tarihi da aka gada daga kakanni ba na kayayyaki ba na farko na kasar Sin.
A garin Akqi, duk wani gida yana da Manas, yara su kan saurari Manas da kaka ko mahaifinsu kan rera a cikin gida. Risbek shi ne dan jikan Mamayi, yawan shekarunsa zai kai 6. Ya bayyanawa 'yan jarida cewa, yana son sauraron Manas, kana yana son rera Manas. Bayan da ya girma, yana fatan zai zama wani mai rera Manas mafi kyau kamar kakan babansa. A makarantar firamare ta garin Akqi, mahaifin wata yariniya mai shekaru 12 ta kabilar Kirgiz Bostan ya bayyana wa 'yan jarida cewa,
" Manas muhimmin abin ne na kabilar Kirgiz. Ta hanyar koyar Manas, yara su kan iya koyar harshan kabilar Kirgiz cikin sauki, kana su kan iya koyar da al'adu da tarihi na kabilar. A matsayin dan kabilar Kirgiz, kamata ya yi yarana su koyi Manas."
Ga 'yan kabilar Kirgiz, Manas ta zama kamar gishiri. Idan babu Manas, babu dadi a zaman rayuwa. Masu rera Manas sun yi amfani da muryarsu mai dadi wajen bada kwarin gwiwa ga dukkan 'yan kabilar Kirgiz, mata ko maza, babba da yaro. Koda 'yan kabilar Kirgiz za su je wuri mai nisa, ko su bar zaman rayuwar kiwon dabobi na dogon lokaci, Manas ta zama muhimmin kashi a cikin zuciyarsu.