Jianger, wani nagartaccen sarki ne Jarumi da ya yi suna a tarihin al'ummar Mongoliya. A lokacin da yake sarautar yankin Mongoliya yau fiye da shekaru dubu 1, ya yi yake-yake da dama domin fadada fadin kasarsa ta Mongoliya da kuma kawo kwanciyar hankali da alheri ga jama'arsa ta Mongoliya. Sabo da haka, a cikin shekaru fiye da dubu 1 da suka gabata, al'ummomin Mongoliya su kan rera wakokin yaba mashi, har ma ya kai ga an rubuta wata doguwar waka mai suna "Janggar".