Daga nan sai Nalati, wani wurin filin ciyayi mai kyan gani. Akwai kananan kabilun wannan yanki masu yawa a wannan wuri amma dai kabilar Kazakh ne mafi akasari. Da yake makiyaya ne, mun zazzaga mun ba idanunmu abinci wajen ganin yadda suke zamantakewarsu da rayuwa. Kana mun ci abincinsu, har ma sarkin wannan yanki da matarsa sun kai mana ziyara don karramawa da kuma ban girma garemu bakinsu. Mun yi rawa tare da su. Abin gwanin ban sha'awa.
A hakikanin gaskiya, gaba dayanmu mun yaba da abubuwan da muka gani, ina iya cewa ayuwa ta inganta sosai a wannan wuri. Masu yawon bude idanu da baki 'yan yawon shakatawa da kuma masu neman karin ilimi zasu amfana sosai da irin wannan yanayi da muka gani a Nalati da ma dukkan sauran wuraren da muka kai ziyara. Kuma, ina iya cewa, gwamnatin kasar Sin tana ba da gudunmmuwa daidai-wa-daida ga al'ummarta wadda ya kamata sauran kasashe masu tasowa da ma wadanda suka ci gaba su yi koyi da kasar Sin din don ci gaba da kuma bunkasa a wannan karni da muke ciki da ma nan gaba.
Ba zan manta kokarin ma'aikatan CRI da kuma ma'aikatar samar da labarai ta kasar Sin ba wajen nuna yabo gare su. Sun burge ni sosai.
Na gode.
Salisu Muhammad Dawanau
2012.07.17