in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An shirya bikin ba da lambobin yabo ga wadanda suka ci gasar "Xinjiang da nake daukar hotonta" a birnin Urumqi
2012-07-17 14:27:02 cri
An shirya bikin ba da lambobin yabo ga masu duba shafin Intanet na gida da na waje da suka ci gasar "Xinjiang da nake daukar hotonta" a birnin Urumqi a ran 11 ga wata da dare. Gasar din kuma gidan rediyon kasar Sin da ofishin watsa labaru na jihar Xinjiang ta Sin su biyu ne suka shirya tare.

A yayin bikin, mataimakin gidan rediyon kasar Sin Xia Jixuan ya bayyana cewa, jerin harkokin da suka shafi gasar "Xinjiang da nake daukar hotonta" sun yi amfani da kafofin watsa labaru na ketare wajen nuna wata Xinjiang ta hakika ga duniya, wadanda suka samu martani sosai daga masu duba shafin Intanet na gida da na waje. Ana fatan wadanda suka ci wannan gasar za su bayyana abubuwan da suka gani kuma suka ji ga dimbin mutane, domin a kara fahimtar jihar Xinjiang.

Hou Hanmin, shugabar ofishin watsa labaru na jihar Xinjiang a nata jawabin ta ce, gidan rediyon kasar Sin na taka muhimmiyar rawa a cikin ayyukan yada labaru ga duniya. Wannan gasar da bangarorin biyu suka hada kai wajen gudanar da ita za ta samar da wata kyakkyawar dama wajen nuna hakikanin jihar Xinjiang da daga kwarjininta a duniya yadda ya kamata.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China