in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An shirya bikin ba da lambar yabo ta musamman ga masu shiga yanar gizo wajen aikin 'Xinjiang da nake daukar hotunanta'
2012-07-17 14:25:58 cri
A daren ranar 11 ga watan Yuli a birnin Urumqi ne, aka shirya bikin ba da lambar yabo ta musamman ga wadanda suka ci gasar nan ta 'Xinjiang da nake daukar hotunanta' a karkashin kulawar gidan rediyon kasar Sin CRI, da ofishin watsa labaru na jihar Xinjiang mai cin gashin kanta. A waje guda kuma, an kaddamar da shirin kai ziyara a Xinjiang da wadanda suka lashe gasar. Yanzu ga cikakken bayanin da abokiyar aikinmu Bilkisu ta kawo mana.

Da wannan kida mai dadin ji na gargajiyar jihar Xinjiang, aka bude bikin ba da lambar yabo ta musamman ga masu shiga yanar gizo ta intanet da suka lashe gasar nan ta 'Xinjiang da nake daukar hotunanta' a otel din Haide dake birnin Urumqi. Zaunanen mamban kwamitin jam'iyyar kwaminis na jihar Xinjiang mai cin gashin kanta, kuma ministan fadakar da jama'a na jihar mista Hu Wei, mataimakin shugaban CRI, mista Xia Jixuan da sauran shugabanni sun halarci bikin, inda kuma aka gayyaci wadanda suka lashe gasar guda 11 da suka fito daga kasashen Sin, Burtaniya, Masar, Nijeriya, Jordan, Turkiya, Iran da dai sauransu.

Da farko, mataimakin shugaban CRI mista Xia Jixuan ya bayyana yadda aka aiwatar da jerin shirye-shiryen game da 'Xinjiang da nake daukar hotunanta'.

'A watan Satumba na shekarar 2011 ne, gidan rediyon kasar Sin da ofishin watsa labaru na gwamnatin jihar Xinjiang mai cin gashin kanta suka samu cikakkiyar nasarar shirya aikin daukar hotuna a jihar Xinjiang tsakanin 'yan jarida masu aikin daukar hotuna da suka fito daga kasashen musulmai, wato 'Xinjiang da nake daukar hotunanta'. Daga watan Disamban shekarar 2011 zuwa watan Feburairun shekarar 2012 kuma, tashoshin intanet na CRI dake amfani da harsunan Turanci, Larabci, Hausa, Persia, Turkiya, Indonesiya da sauransu na gidan rediyon CRI sun hada kai tare da wasu tasoshin intanet na kasar Sin, da wasu na kasashen ketare kusan 20 da suka shiga shirin daukar hotuna don shirya aikin 'zaben hotunan da nake so', inda aka nuna hotuna masu kyau da 'yan jarida suka dauka, inda aka nuna wa duniya surar jihar Xinjiang.'

Aikin 'Zaben hotunan da nake so' da aka shafe watanni biyu ana yinsa ya jawo hankalin masu shiga yanar gizo na gida da na waje da yawa. Bayan da suka kalli hotunan, wasu masu shiga yanar gizo na kasashen ketare sun nuna mamaki kan yanayi mai ni'ima na jihar Xinjiang, sun kuma nuna sha'awa kan yadda zaman rayuwar jama'ar jihar take, har ma sun nuna fatansu na kai ziyara a Xinjiang. Daretkar ofishin watsa labaru na gwamnatin jihar Xinjiang mai cin gashin kanta madam Hou Hanmin tana ganin cewa, aikin 'Xinjiang da nake daukar hotunanta' ya taka muhimmiyar rawa wajen nuna wa duniya game da yadda Xinjiang ta ke, kana da bayyana sigarta mai kyau a duniya.

'A matsayinsa na ginshikin kasar Sin wajen watsa labaru ga kasashen ketare, gidan rediyon CRI ya aiwatar da ayyuka masu muhimmanci wajen bayyana yanayin jihar Xinjiang. Za mu ci gaba da wannan aiki na 'Xinjiang da nake daukar hotunanta'. Bisa fiffikon da CRI yake bayarwa wajen watsa labaru ta harsuna da dama za mu kara bayyana surar garinmu ga al'ummomi daban daban na duniya.'

A cikin masu shiga aikin 'zaben hotunan da nake so', madam Eda Ozsoy da ta fito daga kasar Turkiya ta yi sa'ar samun lambar yabo ta musamman, abin da ya ba ta damar kawo ziyara a jihar Xinjiang, a yayin da take yin jawabi a madadin wadanda suka lashe gasar, ta bayyana cewa,

'Wannan aiki na 'Xinjiang da nake daukar hotunanta'ta samar da wata dama mai daraja don mu kara fahimtar jama'ar kabilu daban daban dake zama a jihar Xinjiang, da kuma al'adun gargajiyar iri daban daban. Za mu gaya wa jama'ar kasashenmu kan abubuwan da muka ji muka saurari game da Xinjiang, don sanya mutane mafi yawa su kara fahimtar Xinjiang, da ma kasar Sin.'

Maxence Melo Mubyazi da ya fito daga Tanzaniya ya yi farin ciki sosai kan ziyarar da yanzu haka yake yi a jihar Xinjiang.

'Wannan ne karo na farko da na zo kasar Sin da kuma jiharta ta Xinjiang. A da na samu labaru game da Xinjiang ne ta hanyar shirye-shiryen da sashen Swahilli ya tsara ta hanyoyin rediyo da yanar gizo. Na yi farin ciki da samun wannan damar ta zuwa Xinjiang. Abinci, yanayi, al'adu da kuma gine-ginen dake jihar dukkansu sun ba ni sha'awa. Ina fatan zan kara fahimtar al'adu da abubuwan musamman na wurin, da kuma koyi da abubuwa mafi yawa a ziyararmu a 'yan kwanaki masu zuwa.'

A cikin kwanaki 6 masu zuwa, wadannan masu shiga yanar gizo guda 11 da suka samu lambar yabo za su kai ziyara a wasu shahararrun yankuna na jihar Xinjiang, ciki har da Turpan, Kanas da kuma Yining. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China