Birnin an kasa shi kashi biyu, saboda haka, bayan an kai mu masauki a bangaren zamani wato inda masu hannu da shuni suke, sai kuma muka kai ziyara unguwannin da masu karamar karfi suke don gane wa idanunmu yanayin rayuwa a can. Mun yi mamaki don unguwar tana da kyau kamar dai ba na masu karamar karfi ba. Suna rayuwa cikin annashuwa da kwanciyar hankali. Ruwan famfo da wutar lantarki da magudanar ruwa da tsarin layuka kuwa abin ba a cewa komai. An zazzaga da mu cikin unguwar kuma mun ga yadda mutanen yankin ke tsara gidajensu ta yadda zai dace da zamantakewa irin na yau. Sai da muka tube takalma kafin mu shiga dakunan wasu gidaje, wannan ya sa na tuna kasar Hausa kuma yadda wasu dokokinmu suke. Mun zazzaga wadannan unguwanni a kan keken dokuna kowa na yaba wa irin ci gaba da ake smu a wannan wuri.
A cikin wannan unguwa muka ci abincin rana, kuma komai muka ci a wurin halal ne don kowane Musulmi na iya cin abincin wurin hankalinsa kwance.
Daga nan sai muka zarce zuwa wani wurin adana kayan tarihi na kabilar Xibo. Kabilar Xibo na daya daga cikin kananan kabilun dake Yining. Mun ga kayayyakinsu na da da kuma irin wadanda suke amfani da su a yau. Kabilar Xibo ta shahara ainun wajen yin amfani da kwari da baka a kasar Sin da ma duniya baki daya. Mun gwada bajintarmu a wannan wuri don kwaikwawonsu amma dai abin da kamar wuya. An kuma yi wasu wakoki da raye-raye wadanda suka burge mu baki daya.
Hakika, gaba dayanmu mun samu sabuwar fahimta game da kananan kabilun kasar Sin da kuma yadda gwamnatocin kasar Sin na baya da na yanzu ke kokari wajen ba dukkan dan kasar hakkinsa a duk inda yake. Wannan abu ne mai matukar kyau da muhimmancin gaske. (Salisu Dawanau)