Daga nan mun wuce zuwa filin jirgin sama na Urumqi zuwa Kanasi. Akasarin mutanen wannan wuri Kanas makiyaya ne na shanu da kuma kananan dabbobi kamar su raguna da tumaki, ban da kuma dokuna da su kan hau yayin kiwo. Da harshen Kazakh 'Jaksma' yana nufin sannu. Ke nan akwai ni'ima a wurin tun da abinda zaka ji ke nan a bakunan mutanen wurin. Kuma kalmar 'Kanas' tana nufin wuri mai ban mamaki ko al'ajabi. Abin haka yake. Mun zazzaga wannan yanki, kuma mun ga abubuwan ban sha'awa da ban mamaki. Kogin Kanas da filayen ciyayi da kuma girman dabbobin da ke yankin na iya ba mai kai ziyara sha'awa da kuma burgewa ta musamman. Abinci mai dadi kuwa sai wannan wuri. Wani abin sha'awa kuma a wannan wuri shi ne irin yadda gwamnatin kasar Sin kan taimaka wa makiyaya wajen samar musu wutar lantarki kyauta saboda harkokin su na yau da kullum. Ka san makiyayi baya zama wuri guda, saboda wannan wani al'amari mai muhimmancin gaske a gare su.
Na yi murna sosai da wannan ziyara, na samu ilimi game da abubuwan da ban san su ba a can baya kuma zan tabbatar sauran 'yan uwana daga Najeriya sun samu wannan bayani ko labari yayin da na koma gida nan da kwanaki masu zuwa.
Na gode kwarai CRI.
Salisu Muhammad Dawanau