in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ziyara a Xinjiang akwai riba
2012-07-15 17:30:54 cri
A ranar Alhamis, 12 ga watan Yuli, Mun kai ziayar wurin da ake kira 'Dutse mai wuta'.Kamar yadda sunan yake, wasu duwatsu ne ko tsaunuka masu ban al'ajabin gaske kuma akwai hasken rana mai kimanin 'degree 50 zuwa 55 a wannan yanki na Turfan na Jihar Xinjiang. Abin mamakin shi ne, muddin yamma ta yi, wadannan tsaunuka ko duwatsu kan zama tanmkar garwashin wuta don kallarsu zai canza ainun. Mun ci abinci rana a inda ake kira 'Koramar Inabi' ko 'Grape Valley'. A wannan wuri ne muka samu bayanain yadda inabi ya fara shiga kasar Sin da dai sauran muhimman bayanai masu ilmantarwa.

Akwai wani abinda muka gani a kan hanyarmu ta zuwa Turpan daga Urumqi da naga ya dace in gaya wa mai sauraron CRI Hausa musamman dan asalin Afirka. Mun yada zango a wani kamfani mai samar da ingantaccen wutar lantarki da yin amfani da karfin iska cikin sauki da kuma araha. Gaskiya, aikin wannan kamfani ya bani sha'awa sosai musamman ganin cewa mu gwamnatocinmu ya kamata su rika koyi da kasar Sin don samar da irin kamfani don samun wuta cikin sauki, tun da mu ma muna da isasshen iska da za'a amfani da shi.

An karramamu mu 11 da muka yi nasara a gasar 'Xinjiang da nake daukar hotonta', kuma yi farin ciki sosai musamman ma ni da yake karo na biyu ke nan. Mun yi murna ainun a wurin wannan muhimmin buki mai kayatarwa. Mun karbi kyaututtukanmu kuma mun dauki hotuna tare da sauran ma'aikata CRI. Hakika, wannan wani abin farin ciki ne da ba zan manta da shi a rayuwana.

Na gode kwarai.

Salisu Muhammad Dawanau

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China