Daga wannan wuri, mun tsaya wani dabki ko kogi mai kyawun gani. Mun zazzaga tsaunuka da kuma cin abinci a don kara fahimtar yadda wannan yanki yake. A wannan tsaunuka, mun ga yadda al'umar Kazakh ke rayuwarsu kasancewar makiyaya ne. mun yadda gidajen su yake da kuma yadda suke zamantakewarsu. Abinda ya bani mamaki a wannan wuri ko a duk inda muka zaga, mutanen kauyukan na yi rubutu da karatu komai tsufarsu, kuma komai kurucuyarsu, ga kuma wutar lantarki kamar a Birnin Abuja ko Ikko. Akwai kuma tsabta, tun da duk inda ka zaga, zaka ga abubuwan zubar da shara. Hakika, na samu karin ilimi a wannan wuri, haka ma sauran wadanda muka kai ziyara tare da su. Mutumin Birtaniya dake tare da mu ya yi ta bamu dariya saboda ya nuna mana cewar bai yi tsammani akwai irin wannan ci gaba ba a wannan wuri. Sauran 'yan ayarinmu su ma sun yi na'am da abubuwan da muka gani.
Ina fata, nan gaba wasu masu sauraron CRI Hausa su ma zasu samu irin wannan dama don kai ziyara kasar Sin don kara ilimi da fahimta.
Kanana kabilun kasar Sin sun burge ni sosai saboda kiyaye doka da kuma inganta yankunansu koda yake gwamnatin tsakiya ta kasar ita ce za a kara yaba mata don kokarinta.
Na gode.
Salisu Muhammad Dawanau