in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Urumqi a idona
2012-07-12 15:51:50 cri
Yau ranar Laraba, 11 ga Yuli, wata rana ce mai dauke da kai ziyara wurare biyu ko uku masu muhimmancin gaske a wannan ziyara tamu zuwa kasar Sin da Jihar Xinjiang. Da farko di mun je gidan adana kayan tarihi(museum) dake nan Xinjiang. Abin ban mamaki, akwai wayewar kai na tsawon shekaru masu yawa bisa ga abubuwan da muka gani, da kuma irin bayanai da aka yi mana. Kuma a ganina, akwai bambanci mai yawa a tsakanin kasashenmu da yadda ake ba wannan bangare muhimmanci. Mun ga wasu gawawwaki da aka adana su tun shekaru sama dari biyu, da kuma na wata mace da idan ka ga gawar za ka dauka bata dade da barin duniya ba saboda hanyoyin da aka bi wajen adanar. Ya kuma nuna mini cewar kan mutanen wannan bangare ya dade da wayewa nesa ba kusa ba. A kasata da wasu bangare na Afirka, na ga yadda su kan ajiye kayayyakin tarihi amma bai kai na nan ba.

Mun kuma kai ziyara a wurin yin ibadar masu addinin Budha. A gaskiya, an kawata wannan wuri ta yadda masu ibada ba za su kuntata ba, haka su ma masu zuwa yawon bude idanu da yin bincike. Wurin yana da kyau da kuma muhimmancin gaske ga kuma ban sha'awa saboda kyawunsa.

Mun kuma zarce zuwa wasu wurare biyu masu muhimmancin gaske. Gidan rediyon na Jihar Xinjiang da kuma gidan talabijin. Wani abin farin ciki da na yi la'akari da shi, kusan duk wani abu matasa ke gudanar da shi, manya sai dai su rika kallo kawai don bada shawara ko kuma inda aka  kuskure sai su yi gyara ba irin yadda abin ke faruwa a wasu kasashe irin namu ba.

A duk wadannan wurare biyu, mun zazzaga inda ake harhada labarai da bayanai, da kuma yin fassara da gabatar da shirye-shirye, wurin da ya ba ni sha'awa shi ne wani daki mai dauke da na'urorin hada labari masu yawan gaske, kuma wadannan na'urori suke sarrafa kansu ba tare da wani ya sanya hannu ba. A nan muna iya cewa, an samu ci gaba sosai a wannan fanni mai muhimmanci. Akwai ayyuka da yawa a wadannan wurare biyu amma na lura akwai kwazo da himma a fuskokin matasa dake gudanar da aiki a wurin. Suna gudanar da fassara labarai da bayanai a harsunan Rashanci da Sinanci da harshen Karkar da na Uygur abin gwanin ban sha'awa.

Gaba daya, ina iya cewa, a wannan jiha akwai son juna da rungumar baki, ga kuma zaman lafiya da annashuwa a duk kan inda mutun ya zaga.

Na gode.

Salisu Muhammad Dawanau
 
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China