in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kai ziyara a Xinjiang
2012-07-11 16:29:56 cri

Yau rana ce mai dauke da abubuwan tarihi kasancewar mun kai ziyara Urumqi dake Lardin Xinjiang ta kasar Sin.

A shafin yanar gizo ta sashen Hausa da ma na sashen Turanci na CRI, an kafe wasu hotuna masu nasaba da gasar da aka gudanar. Hakika hotunan sun kayatar amma a gaskiya ba su nuna zahiri abubuwan ci gaba dake Urumqi ko Lardin Xinjiang.

A yau ina Xinjiang, kuma na yi mamaki ainun da ganin ci gaba da kuma bunkasa da wannan lardi ke da shi. Ga abubuwan more rayuwa ga mutanen wurin, ga kuma tsare-tsare na bunkasa kasa da jama'a. abin sai wanda mutun ya gane wa idanunsa.

Bayan mun huta a masauki, an kai mu wani kamfanin dake gudanar da ayyukan yada labaru nagartattu masu nasaba da nahiyar Asiya, da kasar Sin da ma duniya baki daya. Ana ce ma wannan ma'aikata 'tianshannet.com'. Hakika, a wannan wuri, mun ga yadda ci gaba ke gudana a Xinjiang. Muhimman bayanai ta hanyar yanar gizo da mujallu ko rediyo, wannan kafar yada labarai ke amfani da su wajen yada bayanai masu muhimmanci ga duniya. Mun zazzaga sashe-sashe don gane wa idonmu yadda sasan ke ayyuka, mun kuma yi tambayoyi don kara fahimta. Gaba daya, ofishin kan samar da bayanai da harsuna biyar; Turanci, Kazakh, Uygur, Sinanci da kuma Rashanci. Hakika, an samu ci gaba mai yawa idan muka yi la'akari da samar da bayanai ba tare da muzgunawa ba a wannan wuri.

A gaskiya, Xinjiang na dauke da mutane masu son jama'a da kuma karimci da yakana ga baki da kuma wadanda kan kai ziyara yankin neman karin ilimi ko bincike.

A kamfani na biyu da muka kai ziyara yau, wato kamfani mai suna 'Qarluq Media Technology Limited', mun ga abubuwan ban mamaki da al'ajabi. A wannan kamfani ne ashe kamfanin 'Apple' ke tinkaho wajen sanya wasu bayanai a cikin ayyukansa don nishadantar da jama'a. An zazzaga da mu sashe-sashe na kamfanin don mu ga yadda su kan kirkirui zayyana irin na 'cartoon', har ma an nuna mana zahiri yadda abin yake. Shugaban wannan kamfani na 'Qarluq' tare da wani jami'i sun ba mu nagartattun bayanai game da ayyukan kamfanin, da kuma irin hadin gwiwa dake tsakaninsu da wasu kamfanoni daban daban. Haka kuma sun bayyana mana burinsu a nan da shekaru biyar masu zuwa, da irin abubuwan da suke son gudanarwa cikin wadannan shekaru biyar masu zuwa. Gaba daya, zan iya cewa mun samu wani sabon ilmi da ba mu da shi a can baya game da yadda ake zayyana. Akwai dalibai da yawa masu daukar karatu a wurin.

Mun zarce zuwa wata kasuwa don gane wa idonmu yadda take a wannan birni na Xinjiang. A nan, na yi mamaki ainun. Na lura wannan birni yana da tsawon tarihi, kuma mafi yawa mutanen birnin Musulmai ne, ga su da so da kuma aminta baki. Na yi tattaki ni kadai a cikin kasuwar don sayo wani abu, abin mamaki wani mutun wanda ban sani ba shi ne ya kai ni shago na yi sayayya din.

A gaskiya dai, abin da na yi tsammani game da Xinjiang ba shi na gani ba. Na yi tsammani wurin babu su gaba sosai, amma sai na lura akwai alamar wayewar kai da kuma bunkasa mai yawa; mu'amala, bunkasa ta fannin gine-gine, da zamantakewa da rayuwar jama'a yana da kyau sosai idan muka kwatanta da na wasu kasashen duniya.

A ra'ayina, Xinjiang ya zama wani babban yanki mai cin gashin kansa don tsawon tarihi da kuma bunkasa da yake yi yau da kullum, kuma ba wuri ne da aka bari a baya ba ta fannin ci gaba. Ina kuma fata wasu birane na duniya za su yi koyi da shi don ci gaba.

Na gode.

Salisu Muhammad Dawanau

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China