Mr. Chi Chongqing wanda ke kula da harkokin yawon bude ido a jihar Xinjiang ya ce, bayan da gwamnatin tsakiya ta kasar Sin ta yi taron tattaunawa kan yadda za a kara saurin bunkasa jihar Xinjiang a shekarar 2010, sha'anin yawon bude ido ya samu ci gaba cikin hanzari kwarai. Dimbin 'yan kasuwa sun ziyarci jihar. A waje daya, sauran larduna da manyan jihohi 19 na kasar Sin sun kara karfi wajen bunkasa sha'anin yawon bude ido, har ma sun kara zuba jari a wuraren yawon shakatawa. Sakamakon haka, sha'anin yawon bude ido na jihar ya kama kan hanyar samun bunkasuwa cikin hanzari.
Mr. Chi ya jaddada cewa, za a yi kokarin bunkasa sha'anin bude ido a kokarin mayar da shi muhimmin ginshikin tattalin arzikin jihar Xinjiang. Haka kuma, ana fatan yawan masu bude ido da za su kai ziyara jihar Xinjiang daga sauran sassan kasar Sin zai kai miliyan 80 a shekarar 2015, kuma masu yawon masu bude ido daga ketare zai kai miliyan 2. Sakamakon haka, yawan kudin shiga da jihar za ta iya samu a shekarar 2015 zai wuce kudin Sin yuan biliyan 85.
Jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta, wato jiha ce mai arzikin wuraren yawon shakatawa wadda take makwabtaka da wasu kasashe da yawa da suka hada da yankunan Asiya da Turai. Sakamakon haka, tana da makoma mai haske wajen bunkasa sha'anin yawon shakatawa. (Sanusi Chen)