in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masu sauraron CRI za su kaddamar da ziyararsu a Xinjang(2010-08-01)
2012-07-05 19:05:34 cri
Ran 1 ga watan Agusta, a birnin Urumchi, babban birnin jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta ta kasar Sin, an yi babban taron ba da lambar yabo ta musamman ga masu sauraron gidan rediyonmu na CRI da suka shiga gasar kacici-kacici ta "shiga jihar Xinjiang". Li Yi, shugaban sashen kula da yayata jihar Xinjiang da Ma Bohui, mataimakin babban editan CRI da sauran manyan baki sun ba wa masu sauraro 8 da suka fito daga kasashen Turkey da Masar da Amurka da sauran kasashen waje lambar yabo ta musamman.

Salih Sinan Onus, mai sauraronmu da ya zo daga kasar Turkey ya bayyana cewa, sakamakon karancin labaru daga kafofin yada labaru masu tsaka-tsakin ra'ayi, a kan samu fahimtar kasar Sin bisa ra'ayin kafofin yada labaru na yammacin duniya kullum. Gasar kacici-kacici ta "shiga jihar Xinjiang" ta ba jama'a damar gane wa idonsu yadda kasar Sin da jihar Xinjiang suke kasancewa.

Bayan halartar babban taron, wadannan masu sauraronmu za su kaddamar da ziyararsu ta tsawon mako guda a jihar Xinjiang. (Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China