in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tafiyar masu sauraron CRI a jihar Xinjiang ta kammala tare da samun babbar nasara(2010-08-07)
2012-07-05 19:06:47 cri
A ran 7 ga wata a birnin Urumqi, hedkwatar jihar Xingjiang ta Uygur mai cin gashin kanta, an dasa aya ga aikin "Tafiyar masu sauraron gidan rediyon CRI a jihar Xingjiang", wadanda kuma suka ci gasar kacici-kacici mai taken "Shiga Xinjiang" da gidan rediyon CRI ya shirya.

A yayin da suke jihar Xinjiang, masu sauraron CRI 8 da suka fito daga kasashen waje sun kai ziyara a Urumqi, Turpan, Altay, Shihezi da dai sauran sassan jihar tare da tawagar CRI, ziyarar da ta fahimtar da su kan bunkasuwar tattalin arziki da zamantakewar al'umma na jihar Xinjiang daga duk fannoni. Har wa yau kuma, sun yi musayar ra'ayi da yin shawarwari da shugabannin hukumomin watsa labaru na Xinjiang da kuma 'yan jarida. Wadannan masu sauraro sun bayyana cewa, sun gano wata jihar Xinjiang mai kyan gani cikin lumana ta wannan ziyara, ba za su manta da ita ba har abada.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China