in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ga ra'ayina game da nasara da na yi a gasar Xinjiang, da nake daukar hotunanta
2012-07-05 16:37:07 cri
Gidan Rediyon kasara Sin (China Radio International) ya cika shekaru 60 da kafuwa a karshen shekara ta 2001. A lokacin ne na samu nasara a gasar kacici-kacici da gidan rediyon ya gudanar, har kuma na samu damar kai ziyara kasar Sin. Na yi wannan ziyara ne cikin natsuwa da kwanciyar hankali. A gaskiya, ba zan manta da yanayin da na samu kai na a ciki ba saboda farin ciki da na yi. Na kai ziyara karo na farko, kuma abin yana zuciyata ta har yanzu.

Kwanci-tashi, Allah Ya sake kawo mu wannan lokaci, bayan shekaru fiye da goma. A karshen watan Mayu, 2012, na samu labarin cewar zan sake kai ziyara kasar Sin daga Malama Fatima Liu, wacce ke kulawa da harkokin duk masu sauraron sashen Hausa na CRI. Sannan daga bisani, Shugaban sashen Hausa, Malam Sanusi Chen, ya aiko mini da sakon 'text' game da wannan albishir.

Idan mai sauraron CRI ba zai manta ba, a karshen shekarar 2011 gidan rediyon ya shirya wani gasa game da daukar hotuna a Xinjiang. To, a sanadin wannan gasar ne na sake samun nasara da kuma kai ziyara kasar Sin.

Tun daga ranar da na samu wannan muhimmin labari nake cike da murna da kuma farin ciki. Wani abin farin ciki kuma shi ne, wannan ziyara zai kara bani damar sanin kasar Sin da al'adunsu da kuma wasu muhimman abubuwa na rayuwa. Kuma, zan samu damar ganin yadda aka samu ci gaba a kasar Sin bayan shekaru goma da tafiyata ta farko.

A nan, ina so zan yi kira gare mu baki daya, masu sauraron CRI Hausa. Mu kasance masu mai da hankali da nagartattun shirye-shiryen sashen da kuma bada shawara ko korafi a inda ya dace don sashen ya ci gaba da kyautata ayyuka domin jin dadin mu baki daya. Haka kuma, ya kamata mu kara hakuri da juriya game da ayyukan sashen. Ina ganin haka zai bamu damar fahimtar ayyukan su a koda yaushe.

Hakika, wannan nasara da na yi, tare da sauran masu sauraron CRI na sauran sassa, zai kara mana sani da ilimi game da kasar Sin baki daya. Na yi murna sosai, murna kuma irin wadda ba zan iya misalta girmansa ba.

Na gode.

Salisu Muhammad Dawanau

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China