in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ra'ayinka/ki kan batun da ya shafi cika shekaru 70 da kawo karshen yakin duniya na biyu, da kuma nasarar da Sinawa suka samu kan mayakan Japan
2015-08-20 16:35:04 cri

Shekarar 2015 shekara ce ta cika shekaru 70 da Sinawa suka samu nasara kan mayakan Japan, wadda hakan ya kawo karshen yakin duniya na biyu, don kara sani ra'ayoyin masu saurarommu na ketare kan wannan batu, Gidan Rediyon CRI ya shirya wasu tambayoyi ta intanet, kuma muna fatan masu saurarommu za ku bayyana ra'ayoyinku kan batun.

Tambayoyi: (ban da tambaya ta farko da ta biyu, kuna iya zaben amsoshi fiye da guda daya)

1. Shekarun haihuwa

□ kasa da shekaru 35 □ 35 zuwa 50 □ fiye da shekaru 50

2. Matsayin ilmi

□ takardar shaidar kammala makarantar sakandare ko kasa da haka

□ digiri na farko

□ digiri na biyu

□ digiri na uku

3. Wace kasa ta kuma shirya bukukuwan cika shekaru 70 da samun nasarar kawo karshen yakin duniya na biyu?

□ Faransa

□ Amurka

□ Burtaniya

□ Rasha

□ sauran kasashen sun hada da:______________

□ ban sani ba

4. Mene ne ra'ayinka/ki kan ma'anar shirya wadannan bukukuwa na tunawa da cika shekaru 70 da samun nasarar kawo karshen yakin duniya na biyu?

□ tunawa da tarihi da kuma koyon darussan tarihi

□ hana aukuwar tashin hankalin nuna amfani da karfin soja

□ kiyaye darussan da aka koya bayan samun nasarar kawo karshen yakin duniya na biyu

□ murnar samun nasarar kawo karshen yakin duniya na biyu

□ wasu dalilai_______________

□ ban sani ba

5. Ko ka/ki san ma'anar yarjejeniyar Potsdam?

□ a ranar 26 ga watan Yuli na shekarar 1945, kasashen Sin, Amurka, Burtaniya suka fitar da sanarwar Potsdam dake karkarar birnin Berlin na kasar Jamus inda aka bukaci kasar Japan da ta mika wuya.

□ shelar da aka tabbatar da cewa, yakin da kasar Japan ta tayar ko kadan bai cancanta ba.

□ takarda ce dake tunawa da babbar hasarar da dan Adam ya samu cikin yakin duniya na biyu, kuma ta alamta cewa, tabbas ne adalci tana cin mugu.

□ da sauransu__________

□ ban sani ba

6. Mene ne ra'ayoyin kasashen Japan da Jamus kan yakin da suka tayar?

□ wasu 'yan siyasa na Japan su kan kai ziyara haikalin Yasukuni, har ma ba su amsa laifuffukan yakin da mayakanta suka aikata ba.

□ Japan ta ki amincewa da tayar da yakin hare-hare da bai cancanta ba.

□ tsohon shugaban gwamnatin kasar Jamus Willy Brandt ya durkusa a makabartar Yahudawa dake birnin Warsaw, babban birnin kasar Poland a shekarar 1970, inda kuma ya koyi darasi daga tarihi.

□ shugabannin gwamnatin kasar Jamus sun amince da yakin da bai cancanta ba da Adolf Hitler ya tayar, kana suka nemi gafara daga jama'ar da abin ya shafa.

□ sauransu_________________

□ ban sani ba.

7. Mene ne matsayi da gudummawar da kasar Sin ta bayar a yakin duniya na biyu?

□ kasar Sin ta ba da gagarumar gudummawa wajen yaki da mayakan Japan.

□ kasar Sin ta fi fuskantar yakin a yankin Asiya, ta kuma taimaka matuka a yake-yaken da aka yi a Turai da yankin Pacific, ta kuma ba da goyon baya sosai wajen samun nasarar kawo karshen yakin duniya na biyu.

□ kasar Sin ta ba da babbar gudummawa wajen tsara sabon shirin duniya bayan yakin duniya na biyu.

□ sauransu

□ Ban sani ba.

8. A ganinka/ki. Me ya sa kasar Sin ta samu nasara kan mayakan Japan?

□ Jama'ar kasar Sin sun hada kansu don dakile abokan gaba na kasashen waje.

□ Kasar Amurka ta jefa makamin Atom a kasar Japan.

□ Tarayyar Soviet ta tura sojojinta zuwa yankin arewa maso gabashin kasar Sin.

□ karfin kasar Sin ya karu

□ wasu dalilai__________________

□ ban sani ba.

9. "Tabbatar da zaman lafiya da neman samun ci gaba" shi ne burin al'ummomin kasashen duniya baki daya. A ganinka/ki, ta yaya za a iya magance sake aukuwar yaki a nan gaba?

□ kasashen duniya su mayar da hankulansu kan bunkasa tattalin arziki.

□ kara raya huldar abokantaka ta hanyar sada zumunta da kasashe makwabta.

□ Kasashe su kara karfin tsaronsu da bunkasa fasahohin zamani.

□ MDD ta taka rawa domin tabbatar da zaman lafiya.

□ hanzarta inganta halin da kasashen duniya ke ciki a fannin zaman lafiya da ci gaba.

□ wasu________________

10. Ta wane irin dandalin CRI kake son samun bayanai game da yadda Sinawa ke murnar cika shekaru 70 da samun nasara kan mayakan Japan da kuma kawo karshen ra'ayin nuna karfin tuwo a duniya?

□ Rediyo

□ shafin intanet

□ shirye-shiryen bidiyo

□ shafukan sada zumunta

□ na'urorin tafi da gidanka

□ jaridu ko mujalla

□ sauran hanyoyi_________________

Sharhi kan wasu tambayoyi game da yakin duniya na biyu:

1. A ganinka/ki, bukukuwan murnar cika shekaru 70 da Sinawa ke yi game da nasarar da suka samu kan mayakan Japan da kuma kawo karshen ra'ayin nuna karfin tuwo a duniya yana da ma'ana?

2. Wane irin tasiri kasar Sin ta kawo wa kasarku a shekaru 70 da suka gabata bayan yakin duniya na biyu?

3. Wane irin gudummawa ya kamata kasashen Sin da Japan su bayar wajen inganta halin da ake ciki yanzu a Asiya, da ma duniya baki daya?

Ko akwai wasu shawarwari da za ka bayar kan wannan batu?

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China