in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
JKS ta ba da sanarwar yin kira da a hada kai don yakar maharan Japan
2015-08-13 09:23:44 cri

A rana makamanciyar ta yau wato 8 ga watan Janairun shekarar 1937, kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ya fitar da sanarwa, wadda ke kira da a dakatar da yakin basasa tare da wanzar da zaman lafiya, sanarwar da ta bayyana matsayin jam'iyyar na tashi tsaye wajen yakar maharan kasar Japan, kuma an fitar da sanarwar rabin wata ne bayan da aka daidaita shahararren al'amarin da ya faru ba zato a birnin Xi'an cikin ruwan sanyi.

A ranar 12 ga watan Disambar shekarar 1936 ne kuma al'amarin Xi'an ya faru. Bisa ga yadda Zhang Xueliang da Yang Hucheng suka bukata, Zhou Enlai, da Bo Gu, da kuma Ye Jianying sun isa Xi'an a matsayin wakilan kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, inda suka yi kokarin tilastawa Jiang Jieshi, da ya yaki maharan kasar Japan, tare da daidaita al'amarin Xi'an cikin ruwan sanyi.

Bayan da aka daidaita al'amarin Xi'an cikin ruwan sanyi, a ranar 8 ga watan Janairun shekarar 1937, kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, da kuma gwamnatin Soviet sun fitar da sanarwar kiran daina yakin basasa, inda suka sake jaddada matsayinsu na "daina yakin basasa, da kuma hada kan juna don yakar maharan Japan.

A ranar 10 ga watan Fabrairun shekarar 1937, kwamitin tsikiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ya aika da sako ga cikakken zama karo na 3 na jam'iyyar Kuomintang na 5, inda ya fidda bukatu 5 da tabbaci 4, wato ya bukaci a kawo karshen yakin basasa nan take, domin yin iyakacin kokari wajen yaki da sojojin Japan, da tabbatar da 'yancin magana, da na yin taro, da sakin duk fursunonin siyasa, da kiran taron wakilan sassa daban daban, kamar su rundunar soja, da jam'iyyu da sauransu, a kokarin tattara duk kwararrun Sin domin ceton kasar, da share fagen yaki da sojojin Japan cikin sauri, da kyautata rayuwar jama'ar kasar Sin.

Ban da haka sakon ya ce, idan jam'iyyar Kuomintang ta dauki wadannan bukatu a matsayin manufar kasa, jam'iyyar kwaminis ta Sin ta amince da ba da tabbaci a fannoni hudu, wato kawo karshen aikin hambarar da mulkin jam'iyyar Kuomintang, da canza sunan gwamnatin ma'aikata da manoma zuwa gwamnatin yankin musamman ta jamhuriyyar kasar Sin, da canza sunan jajayen sojoji karkashin jagorancin JKS, zuwa sojojin juyin juya hali na Sin, da gudanar da hakikanin tsarin demokuradiya a yankin musamman, da daina amfani da manufar kwace kasa daga hannu masu kasa da yawa, a kokarin bin tsarin gamayyar al'umma, ta yaki da sojojin Japan yadda ya kamata.

Jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ta samun yabo da karbuwa daga mambobin jam'iyyar Kuomintang masu ra'ayin hadin kai da JKS, da jama'ar kasar, saboda ganin rangwame da JKS ta yi don cimma moriyar al'umma baki daya.

A watan Mayu na shekarar 1937, aka rataya kyallen rubutun kalamai a kofar kudu dake birnin Yan'an, wanda ke yammacin kasar Sin, mai maraba da tawagar sa ido da kwamitin tsakiyar jam'iyyar Kuomintang ta tura. Wannan tawaga a karkashin jagorancin Mr Tu Sizong, ta isa birnin Yan'an ne da zummar kara fahimtar da JKS, game da ra'ayinta na hadin kai da jam'iyyarsa. Hukumomin daban daban na birnin Yan'an sun yi matukar maraba da tawagar, hakan ya kuma kara fahimtar juna tsakanin bangarorin biyu.

Ban da haka kuma, a farkon watan Agusta na wannan shekara, bisa gayyatar da jam'iyyar Kuomintang ta yi masa, kwamitin tsakiyar na JKS ya tura manyan jami'ansa don su halarci taron tsaron kasar, ciki hadda Zhou Enlai, da Zhu De, da Ye Jianying, inda suka ci gaba da yin shawarwari da jam'iyyar Kuomintang.

A ran 22 ga watan Agustan kuma, kwamitin kula da harkokin soja na gwamnatin jam'iyyar Kuomintang, ya ba da umurnin sake tsara jajayen sojoji wato "Red Army", karkashin jagorancin JKS a shekarar 1928, wato zuwa asalin rundunar sojin 'yantar da jama'ar kasar Sin a shekarar 1937. Haka kuma, an sake tsara sojin dake lardin Hunan, da Jiangxi, da Fujian, da Guangdong, da Zhejiang, da Hubei, da Henan, da Anhui, zuwa sojojin dake karkashin jagorancin JKS a yayin yakin kin harin sojojin kasar Japan.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China