in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Li Jin: Likitan kasar Sin mai himmar yaki da cutar Ebola a Saliyo
2015-03-24 15:54:56 cri



Tun barkewar cutar Ebola a yammacin Afrika cikin watan Fabarairun shekarar 2014, gwamnati da sojin kasar Sin sun ba da taimako matuka wajen tinkarar wannan kalubale mai tsanani, sun tura rukunoni har sau 10 zuwa kasashen yammacin Afrika. Yawan masana da masu aikin jiyya da suka turama wadannan wurare ya kai fiye da 1000, matakin da ya samu yabo sosai daga jama'ar kasashen Afrika da kasashen duniya baki daya.

A kwanakin baya, wakilinmu daga CRI ya zanta da shugaban rukunin farko da Sin ta turawa Saliyo kuma wanda ya samu lambar yabo fitaccen likitan Sin dake ba da taimako a kasashen waje, kuma mataimakin shugaban asibiti mai lamba 302 na sojin 'yantar da jama'ar kasar Sin Mr Li Jin, wanda ya bayyana labarinsa a Saliyo, lokacin da yake kokarin ba da taimako wajen yaki da cutar Ebola.

An dai ce yawan al'ummar Saliyo kusan mutane miliyan 6, amma likitoci 'yan kasar ba su wuce 200 ba, kana akwai motocin agaji kwaya 6 kacal, kuma zazzabin cizon sauro, da ciwon kwalara su kan barke a ko wace shekara, abubuwan da suka yi matukar ta da hankalin Li Jin. Ya ce: "Muna gudanar da aikinmu a birnin Freetown, hedkwatar Saliyo, birni ne da babu fitilu masu ba da jagoranci ga zirga-zirga, babu na'urorin daidaita gurbataccen ruwa, ga kuma karancin na'urorin jiyya. Muna aiki a asibitin sada zumunta tsakanin kasashen biyu, wanda Sin ta taimaka wajen ginawa, sai dai dukannin masu aikin jiyya sun gudu saboda rasuwar  wani dake dauke da cutar Ebola a asibitin. Lokacin da muka isa wurin, mun kyautata halin da asibitin ke ciki tun da farko, tare da horar da masu aikin jiyya na Saliyo, ba su da ilimin sa makarin hanci, balle wanke hannunsu, wannan babban kalubale ne gare mu. Ban da haka kuma, masu aikin jiyya na kasar Saliyo dake aiki tare da mu, ba su da ilmin yaki da cutar annoba ko kadan. "

Saboda hakan, asibiti mai lamba 302 na sojin 'yantar da jama'ar kasar Sin ya tura rukunin farko, kunshe da mambobi 30, ciki hadda Li Jin zuwa Saliyo a ran 16 ga watan Satumbar bara, don yaki da wannan mumunar cuta wadda ta fi adabbar mutane a duk wannan karni na 21.

Kafin hakan kuwa, sau da dama hukumar kiwon lafiya ta WHO ta sanar da cewa, ba za a iya dakile cutar Ebola ba a yammacin Afrika musamman ma a Saliyo cikin sauki ba, amma zuwan wannan rukuni ya fidda kasar daga wannan babbar barazana. Mr Li Jin ya bayyana cewa: "A karon farko sojinmu ya tura wani cikakken rukuni na aikin jiyya zuwa kasashen waje, mun isa kasar Saliyo sanye da tufafin soja. Na isa kasar a ranar 1 zuwa 8 ga watan Satumba a zagaye na farko, domin ba da rahoto kan nazari da muke yi a wurin, ga hukumar tsara tsarin kiwon lafiya a safiyar ran 11 ga wannan wata. Kuma a yammacin ranar 12 ga watan, cibiyarmu ta ba da umurnin gaggawa na tura rukuninmu, dake kushe da mutane 30, da wani rukuni na ma'aikata masu nazari zuwa kasar a ran 16 ga wata. Mambobinmu na kunshe da likitoci, da ma'aikatan jiyya, da injiniyoyi, da masu ba da hidima da wasu ma'aikata. Kuma dukkanin ma'aikatan asibitinmu, na shirya mana kayayyaki na rabin shekara, ciki hadda kayayyakin jiyya, da kayayyakin yin rigakafi, da kayayyakin yau da kullum. Ban da haka kuma, akwai bukatar horar da mu, saboda cikinmu babu wanda ya taba ta'ammali da cutar Ebola."

Sakamakon matsalar rashin ingancin harkokin kiwon lafiya a Saliyo, da koma bayan ababen more rayuwa, Li Jin da ma'aikatansa, na sufurin kayayyaki cikin ruwan sama kamar da bakin kwarya, sun kuma kyautata halin asibitin cikin garjin rana, tare kuma da horar da masu aikin jiyyar wurin, wadanda ba su da irin wannan ilimi ko kadan.

Cikin makonni biyu kacal, sun fara karbar mutane da ke dauke da cutar Ebola, karkashin kokarin da suka yi, asibitin ya zama mai karbar marasa lafiya mafi yawa.

Li Jin ya kara da cewa, asibitin ya kai matsayi na biyu a karbar mutane bayan zuwansu da kwanaki 40 kacal. Ya ce: "Saliyo wani dandali ne na kasa da kasa, mutane da dama na gudanar da ayyukansu a wurin, ciki hadda Amurkawa, da 'yan Birtaniya, da Turawan Canada, da 'yan Afrika ta kudu da sauransu. Bayan ga kayayyakin tallafawa da Sin ta samar, a daya hannun ta tura likitoci, da ma'aikatan jiyyarta zuwa kasar. Ban da haka, Sin ta ba da taimako wajen gina wani asibiti a wurin. Kuma ko da yake kasashen Turai ma sun samar da kudade ko kayayyakin aiki, sai dai ba su tura masanansu a wannan fanni zuwa kasar ba. Saboda ganin hakan, shugaban kasar Saliyo ya ce 'ya kamata a koyi yadda kasar Sin ke yi ta fuskar baiwa kasashen Afrika taimako.' Mun karbi mutane marasa lafiya daga ran 1 ga watan Oktoba, ya zuwa ran 16 ga wata Nuwamba, yawan mutanen da muka karba ya kai 274, kuma daga cikinsu 145 an tabbatar da kamuwarsu da cutar, kuma mutane 86 sun rasu. Asibitinmu ya karbi mutane mafiya yawa a Saliyo, tun lokacin da muka isa, kuma babu wasu masu aikin jiyya na Sin ko Saliyo da suka kamu da cutar."

A matsayin shugaban rukunin farko da Sin ta tura Saliyo don yaki da Ebola, ban da ba da kulawa ga jama'ar wurin, Li Jin ya nuna kulawa sosai game da lafiyar masu aikin jiyya. Ban da masu aikin jiyya 30 da Sin ta tura wurin, akwai kuma jama'ar wurin kimanin 100. Wadanda Li Jin ya horar sosai a fannin hana kamuwa da cutar.

A cikin aikinsu na tsawon watanni biyu, babu wani ma'aikacin kasar Sin ko Saliyo ya kamu da cutar. Li Jin ya yi bayani cewa, dukkan likitoci, da ma'aikatan jiyya sun yi aiki karkashin dausayi dake da digiri fiye da 30 a ma'aunin celcius, kuma sun sanya makarin hanci, da na idanu, da murfin takalma. Bayan kammala aikinsu, ana fesa musu magunguna don kashe kwayoyin cuta, sannan a kwashe mintoci 20 wajen cire tufafin ba da kariya har guda 11, duk da wahalar hakan, dukkan likitoci, da ma'aikatan jiyyarmu sun gudanar da wannan aiki cikin nutsuwa. Dadin dadawa, masu aikin jiyya suna shiga dakunan kwanciya sama da sau uku dake cike da kwayoyin cuta, da abubuwan masu dauke da nau'oin ruwan jikin marasa lafiyar, suna kula da gawawwaki, har ma wani lokaci su duba marasa lafiya dake fita farfajiyar wurin killace su kusa da itatuwa, ba da umarnin masu aikin jiyya ba. Su kan bincike su, su kuma samar masu da magunguna. Duk wadannan matakai masu inganci da masu aikin jiyya suka dauka sun yi amfani sosai wajen kubutar da wadanda suka kamu da cutar, da hana yaduwar Ebola a wurin. Mr Li Jin ya kara da cewa: "A matsayina na soja, babu wani dalili na yin fargabar zuwa Saliyo, amma na fuskanci matsin lamba sosai a matsayi na shugaba. Lokacin da shugabanni, da iyalanmu ke ban kwana da mu a filin saukar jiragen sama, na taba fadin cewa 'ba zan koma kasar Sin ba, muddin wani daga ma'aikatana ya kamu da cutar, lallai zan lura da shi.' Na dauki matakai uku: Na farko tsai da manufofi masu kyau cikin ayoyi fiye da 200, don tabbatar da ayyukanmu sun gudana yadda ya kamata. Na biyu kuma, horar da ma'aikatan Saliyo bisa lura matuka, ba za su iya gudanar da aiki ba, sai sun cimma nasarar jarrabawa. Na karshe kuwa mun kara karfin sarrafa ma'aikatummu, saboda ban da Ebola, akwai sauran cututtukan annoba a wurin, kamar su zazzabin cizon sauro da mura da sauransu. Ko da yake, akwai zafi sosai, na hana dukkan ma'aikatanmu sanya gajeren wando idan sun fito da dare."

Saboda da ganin kwarewarsu da ingancin ayyukansu, jama'ar Saliyo da ma'aikata a wannan fanni na kasashen waje sun yaba musu sosai, ban da haka kuma, ma'aikatan kasashen Turai, da Amurka, sun darajanta ayyukan da ma'aikatan kasar Sin suka gudanar, bayan sun kai ziyara a asibitin sada zumunci tsakanin Sin da Saliyo. Hakan ya sa ake tambayar cewa ko rukunin da zai maye gurbinsu, zai gudanar da ayyuka masu kyau kamar na wannan rukuni? game da hakan Li Jin ya bayyana cewa, bayan kammalar aikinsu, za su tattara fasahohi da dabarunsu domin horar da rukunoni masu zuwa.(Amina)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China