in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Zhang Yueming
2015-03-10 14:57:23 cri

Zhang Yueming

Namiji

Mataimakin daraktan sashen kula da mata da mata masu juna biyu na farko na jami'ar Suzhou, kuma mataimakin darektan likita

Shekarun da ya yi yana aiki a ketare: 2012.06-2014.06

Tarihinsa: Zhang Yueming, sakataren rukunin likitoci karo na 11 na kasar Sin dake Guyana, kuma likita ne mai kula da mata da mata masu juna biyu. A yayin da yake aiki a asibitin Geogre Town, ya samu nasarori da dama da ba a taba ganin irinsu ba a tarihin likitanci a wannan kasar, inda ya samu amincewa daga wajen al'umomin wurin, asibitoci da kuma ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar, sakamakon kwarewarsa a fannin likitanci da Turanci, da kuma nuna himma kan aikinsa. Bayan watanni hudu da ya isa Guyana, bayan nazarin da ma'aikatar kiwon lafiyar kasar, da asibitin Geogre Town suka yi, an nada shi darektan sashen kula da mata da mata masu juna biyu na asibitin, kuma mamban hukumar ba da shawara kan likitanci na asibitin, kuma mamban kwamitin kula da harkokin rasuwar mata masu juna biyu da na masu nakuda. Haka kuma ya kula da ayyukan sashen kula da mata da mata masu juna biyu na asibitin Geogre Town a dukkan fannoni, da kuma shiga ayyukan tsara manufofin kiwon lafiyar kasar yadda kamata. A yayin da yake kan mikaminsa, Zhang da ma'aikatan rukuninsa sun gudanar da iyakacin kokari, har ma sun cimma wani matsayi na bajinta, wato yawan mata masu juna biyu da na masu nakuda da suka rasa rayukansu ya kai matsayi mafi kankanta a tarihin asibitin. Nasanar da suka samu ta sanya alkaluma a wannan fanni a duk kasar baki daya sun ragu sosai, ta yadda karon farko ne kasar ta cimma burin muradun karni na MDD a shekarar 2013, hakan dai ya sa Zhang ya samu karramawa daga wajen gwamnatin kasar Guyana, da jama'a, da ma kafofin watsa labarun kasar. Ban da wannan kuma, Zhang ya zama malamin ba da jagoranci kan ayyukan horar da likitoci na ma'aikatar kiwon lafiyar Guyana, inda ya ba da darusa na musamman kan batutuwan da suka shafi ilmin kula da mata da mata masu juna biyu. Haka zalika Zhang ya kan je yankunan karkara masu nisan gaske tare da ma'aikatan rukuninsa, don ba da jinya kyauta ga jama'ar wuraren, da kuma ba su magunguna, lamarin da ya ba shi sunan "mutumin da ke da farin jini ga jama'a" a wannan kasa. Kwarewarsa da kuma manyan nasarorin da ya samu, sun sanya Zhang ya samu yabo da girmama sosai daga wajen gwamnatin kasar Guyana, har ma kafin ya koma kasar Sin, ma'aikatar harkokin wajen kasar ta ba shi lambar yabo.(Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China