in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Zhai Wenliang
2015-03-10 09:17:58 cri

Zhai Wenliang

Namiji

Kwararren likita, kuma direkta mai kula da ciwon kashi, a sashe na uku na asibiti mai lamba 175 na sojin 'yantar da jama'ar kasar Sin.

Shekarun da ya yi yana aiki a ketare: 2013.01-2014.01

Tarihinsa: Dr Zhai Wenliang ya jagoranci rukunin likitocin soja karo na 16 mai taimakawa kasar Zambiya, ya kuma ba da jagoranci ga masu aikin jiya guda 10, wajen gudanar da aikinsu a babban asibitin sojin kasar Zambiya daga watan Jarairu na shekarar 2013 zuwa watan Jarairu na shekarar 2014. Sakamakon rashin na'urorin zamani a fannin aikin kiwon lafiya, da sauran matsaloli a wurin, Dr Zhai ya yi kokari koyar da dabarun kiwon lafiya, da na inganta fasahohin aikin jiyya, ya kuma rubuta littafin dabarun ba da jiyya a Zambiya, inda ya yi bayani a fannoni daban-daban, na sa kaimi ga aikin jiyya da za a yi amfani da su a nan gaba.

Cikin shekara daya da ya yi aiki a kasar Zambiya, Dr Zhai ya gudanar da bincike a karon farko kan hanji, ya kuma farfado da wasu na'urorin jiyya dake wurin. Ban da haka ya kuma cimma nasarar kafa wasu na'urorin bincike na zamani a fannoni daban-daban. Dadin dadawa, ya cimma nasarar gudanar da tiyata 38, tare da ba da jiyya ga mutane fiye da 100 a fannin ciwon kashi.

Kwarewar da Dr Zhai ya nuna ta shaida burin kasar Sin na ba da taimako ga Zambiya, tare kuma da bayyana tunanin hadin gwiwa na sojin kasar Sin, matakin da ya ba shi damar samun yabo, da amincewa kwarai daga ofishin jakadancin kasar Sin dake Zambiya, da Sinawan dake zaune a kasar Zambiya, tare da samun yabo daga gwamnatin kasar. (Amina Xu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China