in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wang Jing
2015-03-10 08:21:08 cri

Wang Jing

Mace

Darektar nas nas a asibitin sada zumunta na birnin Beijing

Shekarun da ta yi tana aiki a ketare: daga watan Agusta na shekarar 2014

Tarihinta:Malama Wang Jing wata nas ce da ke cikin tawagar likitoci da kasar Sin ta tura zuwa kasar Guinea a karo na 24. Bisa ga son ranta ne ta bukaci zuwa Guinea don taimakawa al'ummar kasar. A yayin da take kasar ta Guinea, ta gudanar da ayyuka da dama da suka hada da sakatariya da ilmantarwa da kuma kashe kwayoyin cuta. A matsayinta na sakatariyar tawagar da ke kula da aikin kashe kwayoyin cuta, ta kan jagoranci ma'aikatan wannan tawagar wajen gudanar da aikin kashe kwayoyin cuta, inda a kan gan ta cikin rigar maganin kwayoyin cuta tare da daukar na'urar kashe kwayoyin cuta mai nauyin fiye da kilogiram 10, a baya tana ta fesa maganin kashe kwayoyin cuta, duk da yanayi mai zafi da damshi da ake ciki. A matsayinta na sakatariyar wannan tawagar, tana kuma shan aikin rubuce-rubuce, domin malamar an dora mata nauyin rubuta abubuwan da aka tattauna kansu a wajen taron da kuma rubuta rahoto game da harkokin da tawagar ta ke gudanarwa. A yayin da ake fama da cutar Ebola, an rarraba mambobin tawagar likitocin zuwa rukunonin biyu, don su gudanar da aiki a asibitin sada zumunci tsakanin Sin da Guinea, kuma an sanya malamar cikin rukuni na biyu. Duk da haka, yayin da take hutu, ta kan je dakin tiyata na asibitin, don yin musanyar ra'ayi da majiyyatan wannanasibiti da ke aiki a dakin tiyata, tare da bayyana wa abokan aikinta masaniyarta game da aikin jiyya, lamarin da ya ba ta damar samun yabo sosai daga majiyyatan kasar Guinea.(Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China