in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Zhao Yongjun
2015-03-09 15:47:19 cri

Zhao Yongjun

Namiji

Kwararren likitan babban asibitin birnin Dandong na lardin Liaoning

Shekarun da ya yi yana aiki a ketare: 2006.12-2010.07

Tarihinsa: Zhao Yongjun ya yi aikin taimakon jiyya a ketare sau biyu wato a asibitin Ip Nasser da kuma asibitin juyin juya hali na Tazi da ke kasar Yemen, a matsayin memban tawagar jiyya kana shugaban tawagar daga watan Disamba na shekarar 2006 zuwa watan Yulin shekarar 2010. A halin yanzu, yana shiryawa sosai dan gudanar da aikin ba da jiyya a karo na uku da zai yi a kasar Yemen.

A yayin da yake aiki a asibitin Ip Nasser, likita Zhao ya yi aikin tiyatan mafitsara tare da wata ma'aikaciyar jiyya. A cikin shekaru biyu, likita Zhao ya tuba marasa lafiya fiye da 6000, kuma ya yi aikin tiyata kimanin 400.

Domin karfafa fasahohin jiyyar likitoci da raya aikin ba da jiyya a kasar, likita Zhao ya gayyaci likitocin Yemen a lokacin da ya ke tiyata domin kara musu sani da kuma fasahar aikin jiyya.

A shekaru da dama da ya kwashe yana wannan aiki, ya fuskanci yanayi masu tsanani, kamarsu tsaunuka mai karancin iskar shaka da kuma yankuna masu nisa, likita Zhao ya haye wahaloli tare da jama'ar kasar Yemen.Wannan ya sa ya samu karbuwa da girmamawa sosai daga jama'a, kuma ya samu lambobin yabo da dama a asibitocin kasar sabo da da'a da kwarewarsa

Yanzu, kasar Yemen na cikin halin kiki-kaka. Zhao Yongjun na shirya shugabantar reshen kungiyar jiyya wajen gudanar da aikin taimakon jiyya karo na 3 a kasar Yemen.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China