in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Li Jin
2015-03-09 15:44:23 cri

 Li Jin

 Namiji

 Mataimakin shugaban asibitin rundunar sojojin 'yantar da jama'ar kasar Sin ta 302, wanda matsayin kwarewarsa ya kai drektan likita

      Shekarun da ya yi yana aiki a ketare: 2014.09-2014.11

 Tarihinsa: Bayan da annobar cutar Ebola ta barke a yammacin Afirka, sai asibitin da Li Jin yake aiki ya kafa wata tawagar likitoci cikin sauri don tallafawa kasar Saliyo a kokarin hana yaduwar cutar ta Ebola. Li Jin, wanda aka dauka masa nauyin aiki a wani yanayi na kota-kwana, ya zama shugaban wannan tawagar likitoci ta farko da kasar Sin ta tura wa kasar Saliyo. Sa'an nan ya gudanar da aikin dakile cutar Ebola a kasar daga ranar 16 ga watan Satumba zuwa ranar 16 ga watan Nuwamba na shekarar 2014. A yayin da suke kasar Saliyo, Li Jin ya jagoranci mambobin tawagar inda suka nuna jan hali da haye duk wasu wahalhalu, ta yadda suka kammala ayyukansu yadda ake bukata, gami da daukaka matsayin kasar Sin a idanun al'ummar kasashen duniya.

Li Jin, ya yi amfani da kwarewa da fasahohin da aka amfani da su wajen dakile cutar SARS, murar tsuntsaye da dai sauran manyan cututtuka masu tsanani, inda ya jagoranci tawagar likitocin kasar Sin a kokarin yin gyara fuska ga asibitin, tabbatar da tsarin kula da wadanda suka kamu da cutar Ebola, horar da likitocin kasar Saliyo, da bullo da ka'idojin aiki.

A karkashin jagorancin Li Jin, an yi kwaskwarima ga wani asibiti cikin mako guda kawai inda za a rika amfani da shi wajen karbar wadanda suka kamu da cutar Ebola, haka kuma an yi amfani da hanyoyi daban daban don koyar da likitocin kasar Saliyo fasahar hana yaduwar cututtuka, da magance kamuwa da cututtukan da ke yaduwa. Haka zalika an tsara wasu ka'idoji 243 don tsara yadda za a kula da magani, da tinkarar yanayin kowa ta baci da dai makamantansu.

Ban da haka kuma, yayin da yake kasar Saliyo, Li Jin yana zuwa asibiti a ko wace rana, kuma ya shiga cikin dakunan wadanda suka kamu da cutar Ebola a ko wane mako, inda yake ba da jagoranci, gami da gudanar da aikin jinya da kansa, lamarin da ya burge abokan aikinsa sosai.

Bayan da suka shafe watannin 2 suna gudanar da aikin jinya a kasar Saliyo, tawagar da Li Jin ke jagoranta ta cimma wani matsayin bajintar aiki na karbar mafi yawan mutane a rana daya, gami da kebe masu fama da cutar Ebola mafi yawa a asibiti. Kana cikin masu aikin jinya na kasar Sin da na kasar Saliyo, babu wanda ya kamu da cutar Ebola a tsakanin wadannan watanni 2.

Bisa nasarorin da suka cimma, Li Jin da mambobin tawagarsa sun taimaka wajen zurfafa zumuncin da ke tsakanin Sin da Saliyo.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China