in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yu Lecheng
2015-03-09 10:08:51 cri

 Yu Lecheng

 Namiji

 Kwararren likita, kuma mataimakin diraktan cibiyar kawar da ciwon hanta a asibiti mai lamba 81 na rundunar soji na Nanjing.

 Shekarun da ya yi yana aiki a ketare: Janairun shekarar 2012, zuwa Janairun shekarar 2013.

 Tarihinsa: Tun daga ranar 11 ga watan Janairun shekarar 2012, zuwa ran 30 ga watan Janairu na shekarar 2013, ya yi aiki a matsayin kwararren likita a kasar Zambiya. An nada Yu Lecheng mukamin shugaban tawagar likitocin soja karo na 15 da kasar Sin ta tura zuwa kasar Zambiya. A lokacin da yake aiki a kasar ta Zambiya, Mr. Yu Lecheng ya shawo kan matsaloli iri daban daban, wadanda suka jibanci aiki, da zaman rayuwa. Duk da cewa likitocin kasar Zambiya ba su da kware matuka, kuma na'urorin da suke amfani da su a asibitocin kasar ba na zamani ba ne, da isarsa asibitin kasar Zambiya, Mr. Yu Lecheng bai jira ko dogaro da wani ba, sai ya soma aikin daidaita, da kuma gyara na'urorin asibitin kamar na CT da DR da sauransu. A waje daya kuma, duk da cewa bai iya harshen Turanci sosai ba, nan da nan shi da sauran likitocin kasar Sin sun kammala aikin fassara bayanai, game da yadda ake amfani da magungunan da kasar Sin ta samar ga kasar Zambiya kyauta, sannan kuma suka horar da dimbin likitocin kasar ta Zambiya.

Duk da dimbin aikin da yake sha a asibiti, Mr. Yu Lecheng ya kuma tallafawa Sinawa wadanda suke zaune a kasar ta Zambiya, wadanda ko dai suka samu raunuka, ko kuma suka kamu da wasu cututtuka.

Sakamakon hakan, ya samu yabo da amincewa kwarai daga ofishin jakadancin kasar Sin, da Sinawan da ke zaune a kasar Zambiya. Bugu da kari, Mr. Yu Lecheng da tawagar likitocin kasar Sin dake karkashin jagorancinsa, sun samu yabo daga bangaren kasar Zambiya. Har ma ma'aikatar tsaron kasar ta ba shi "lambar yabo ta hadin gwiwar kasa da kasa". Kaza lika ministan tsaron kasar Zambiyan ya karrama shi da lambar yabo ta "manzon sada zumunta". (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China