141231cha.mp4
|
Zangonmu na karshe shi ne jihar Ningxia mai cin gashin kanta ta kasar Sin, inda a karshe muka sha abin da kowa ya san Sinawa da shi, wato shayi. Sai dai wannan shayi na musamman ya shahara ne saboda ya banbanta da sauran shayi da kowa yake tunani, wannan ana hada shi ne da kayayyakin alfarma guda takwas da suka hada da busashshen inabi, ridi da dai sauran su. Dom haka ake kiran shi shayi mai kayayyakin alfarma 8.