Jama'a masu kallon mu da kuma sauraron mu, barkan mu da war haka barkanmu da sake saduwa a wannsn shirin Kwadon Baka…. To kamar yadda kuka sani a watannin baya mun zagaya cikin kasar Sin, musamman muka ziyarci gundumomi ko in ce wuraren dake da yawan musulmai Sinawa muka ga al'adunsu a bangaren abinci. Da yadda ko wane abinci shi ke bayyana sigar al'adun shin a gargajiya da aka gada tun iyaye da kakanni.
Zangonmu na karshe shi ne jihar Ningxia mai cin gashin kanta ta kasar Sin, inda muka ci naman rago da ake turarawa kamar dai yadda ake turara dambun a kasar Hausa. Wato steamed lamb.